Jam’iyyar NNPP na so a Cafke Atiku, Tinubu, a Hana su takarar Shugaban kasa
- Jam’iyyar NNPP da ake yi wa kirari da mai kayan marmari tana so a hana PDP da APC takara
- Shugaban NNPP na Katsina yace bai kamata Atiku Abubakar da Bola Tinubu su nemi mulki ba
- Sani Litti yace wadannan jam’iyyu sun kashe kudin da ya wuce kima wajen fitar da ‘yan takara
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Katsina - Jam’iyyar NNPP ta reshen jihar Katsina tayi kira ga hukumar zabe na kasa watau INEC ta hana Atiku Abubakar da Bola Tinubu neman shugabanci.
Rahoton da muka samu daga gidan talabijin na AIT ya bayyana cewa shugaban NNPP, Sani Litti yayi wannan kira da ya zanda da ‘yan jarida a Katsina.
Shugaban NNPP na reshen jihar ta Katsina ya zargi manyan jam’iyyun APC da PDP da kashe makudan kudi wajen zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa.
Sani Litti yake cewa jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai hamayya sun saba dokar kudi a lokacin gudanar da zaben fitar da ‘yan takararsu na zabe mai zuwa.
EFCC da DSS su dauki mataki
Baya ga haka, Litti ya yi kira ga hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta cafke Tinubu mai takara a APC da takwaransa na PDP watau Wazirin Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pulse ta rahoto shugaban na NNPP yana rokon jami’an DSS da 'yan sanda su kama wadannan ‘yan takara da duk ‘yan jam’iyyun da suka shiga zaben gwani.
Wasu suna ganin a cikin Atiku Abubakar da Tinubu za a samu wanda zai yi nasara a zaben 2023.
Jawabin Sani Littti
“Muna kira ga INEC ta hana Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu shiga takarar shugaban asa a zaben 2023.”
“Sannan EFCC, ‘Yan Sanda da DSS duk suka kama su, da sauran wadanda suka taka rawar gani wajen zabensu.”
- Sani Litti
A wajen taron Litti ya bukaci majalisar tarayya ta tunbuke Muhammadu Buhari daga kan mulki muddin shugaban kasa ya ki yin murabus saboda matsalar tsaro.
Hakan na zuwa ne a lokacin da aka ji Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yana cewa suna sa ran NNPP za ta lashe zaben gwamnan Kaduna da na sauran kujeru.
Ziyarar 'Yan NNPP zuwa Zazzau
Kun ji labari Rabiu Musa Kwankwaso da wasu jagororin jam’iyyar NNPP mai kayan marmari sun gana da shugaba NEF watau Farfesa Ango Abdullahi a gidansa.
A baya an taba ji tsohon Shugaban Jami’ar ta ABU Zaria, yana yabon ‘Dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya nuna ya fi ‘yan takaran APC da PDP dama-dama.
Asali: Legit.ng