El-Rufai, Zulum, Gwamnoni 10 da suka Bada Hutun Musamman Domin Yin katin zabe

El-Rufai, Zulum, Gwamnoni 10 da suka Bada Hutun Musamman Domin Yin katin zabe

  • Kwanaki hudu suka rage a dakatar da yin rajistar katin kada kuri’a watau PVC a fadin Najeriya
  • Akwai dubban mutanen da ba su mallaki katinsu ba, alhali sun isa munzalin yin zabe a doka
  • A dalilin haka wasu Gwamnoni suke bada hutu na musamman da nufin a karasa wannan rajista

A wannan rahoto da za a karanta, Legit.ng ta tattaro jerin Gwamnonin da suka bada takaitattun hutu a jihohinsu domin ma’aikata da sauran mutane su samu PVC.

1. Kaduna

A ranar Talata aka samu labari Nasir El-Rufai ya bada hutun kwanaki (Laraba zuwa Juma’a) domin a tanadi PVC. Hutun ya zo daidai lokacin da NLC ta ke zanga-zanga.

2. Neja

A karshen watan Yuni aka samu labari Gwamna Abubakar Sani Bello ya bada sanarwar hutun kwanaki biyu domin jama’a su karasa rajistar katin zabe a INEC.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

3. Ogun

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwanaki Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun ya bada sanarwar hutu saboda mutane su iya yin zabe a 2023. Sanarwar ta fito ne ta bakin sakataren labarai, Kunle Somorin.

4. Bauchi

Ranar 27 ga watan Yunin 2022 ya kasance hutu ga mutanen jihar Bauchi. Gwamna Bala Mohammed ya yi wa ma'aikata uzuri a lokacin domin su mallaki PVC.

5. Osun

Gabanin zaben Gwamna a Osun ne aka ji Mai girma Adegboyega Oyetola ya bada damar a ki zuwa aiki wata ranar Juma’a saboda rajistar CVR da karbar PVC.

Wasu Gwamnoni
Gwamnonin Legas, Ogun da Neja
Asali: UGC

6. Filato

Shi ma Gwamna Simon Bako Lalong bai dauki lamarin da wasa ba, ya zabi ranar 27 ga watan Yunin da ta wuce a matsayin hutu saboda jama’a su yi rajistar PVC.

7. Zamfara

Wani Gwamna da ya bada hutun mako daya a jere shi ne Mai girma Bello Matawalle. Daga Litinin har Juma’a aka dauka ba a zuwa wajen aiki saboda kowa ya samu PVC.

Kara karanta wannan

Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata

8. Borno

Bayan Sanata Kashim Shetimma ya samu tikiti a APC, sai aka ji Farfesa Babagana Zulum ya ayyana 21 da 22 na watan Yulin a matsayin hutu domin a kada kuri'a.

9. Yobe

A jerin akwai Mai Mala Buni wanda a karshen watan jiya ya amince ayi kwanaki uku ba tare da an je aiki ba, makasudin hakan shi ne adadin masu zabe ya karu.

10. Legas

Duk da mutane fiye da 500, 000 sun yi rajistar sabon katin zabe a Legas, Gwamna Babajide Sanwo ya bada hutun kwanaki biyu domin a samu saukin rajistar zabe.

An bar Arewa a baya

Dazu kun samu labari cewa har zuwa yanzu, a Kano karin mutane 500,207 kadai aka yi samu a cikin masu zabe, bayan akwai kusan mutum miliyan 15 a jihar.

A Legas akwai sama da mutum 508, 000 da suka shiga rajistar INEC na zaben 2023. Bayelsa mai mutum miliyan 2 kuwa ta na gaban Neja, Sokoto da Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng