NNPC yayi karin-haske kan batun korar Ma’aikata 500 tun da kamfani ya canza tsari

NNPC yayi karin-haske kan batun korar Ma’aikata 500 tun da kamfani ya canza tsari

  • Kamfanin NNPCLimited ya fitar da jawabi na musamman a game da batun sallamar ma’aikata
  • Mai magana da yawun NNPCLimited, Garba Deen Muhammad yace babu wanda aka kora daga aiki
  • Garba Deen Muhammad yake cewa dokar PIA ta tabbatarwa ma’aikata aikinsu da kuma albashinsu

Abuja - Kamfanin mai na kasa watau NNPCLimited, ya karyata rade-radin da ke yawo a gari na cewa akwai shirin da ake yi na sallamar ma’aikata.

A ranar Talata, 27 ga watan Yuli 2022, Nigerian National Petroleum Company ya bada sanarwar cewa babu wani ma’aikacin da yake shirin rasa aikinsa.

Kamfanin ya tabbatar da wannan a wata takaitacciyar sanarwa da Legit.ng ta gani a shafin Twitter.

Mai magana da yawun bakin kamfanin na NNPC Limited, Garba Deen Muhammad ya fitar da wannan sanarwa, yana musanya jita-jitar da ta shiga gari.

Kara karanta wannan

Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata

Garba Deen Muhammad yake cewa kamfanin bai da niyyar korar kowa saboda ya canza salon gudanarwa, ya zama cikakken kamfani na kasuwanci.

Kakakin kamfanin man kasar ya kara da cewa dokar PIA ta shekarar 2021 tayi fayataccen bayani cewa babu wani ma’aikacin da za a kora a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NNPC Limited
Mele Kyari, Buhari da Timipre Sylva Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Haka zalika kamfanin ya ce babu wanda za a ragewa albashi saboda dokar PIA ta fara aiki.

Premium Times ta kawo wannan rahoto, ta karyata maganar da ake yi cewa za ayi waje da ma’aikata 500, har an yi masu tanadin kudin ritayar dole.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na sa rai canje-canjen da aka yi a NNPP zasu kawo gyara.

Jawabin Garba Deen Muhammad

“NNPC limited bai da niyya kuma bai kori ko ma’aikaci daya ba a dalilin sauyawar da ya yi daga hukumar Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) zuwa kamfanin NNPCLimited.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

“Dokar harkar mai ta PIA na shekarar 2021 tayi bayani karara cewa babu wani ma’aikaci da zai rasa aikinsa ko ya karbi kasa da abin da yake karba kafin ayi wannan sauyi.” - Garba Deen Muhammad.

Babu kudi a Najeriya?

A makon jiya aka samu labari Gwamnatin Tarayya ta fitar da rahoton tattalin arziki na farkon shekarar nan, daga Junairu zuwa karshen Afrilu.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed tace biyan bashin da aka yi, ya fi kudin da aka samu a farkon shekarar bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng