INEC: Yadda aka bar Jihohin Arewa a Baya Wajen Rajistar Sabon Katin yin Zabe

INEC: Yadda aka bar Jihohin Arewa a Baya Wajen Rajistar Sabon Katin yin Zabe

  • A karshen watan Yulin nan ne hukumar INEC za ta daina yi wa mutane rajistar sabon katin zabe
  • Alkaluma sun nuna jihohin Arewa sun yi wasa da rajistar, mutane da-dama ba su mallaki katin ba
  • Bisa dukkan alamu an fi ba rajistar karfi a Kudancin Najeriya yayin da ake jiran zabe mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nigeria - Nan da kwanaki hudu rak za a daina yin rajistar sabon katin zabe watau CVR a Najeriya. A jihohin Arewa, mutane sun yi sake da lamarin.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a yau Laraba, ta nuna cewa an bar jihohin yankin Arewa a baya, musamman idan aka yi la’akari da yawan mutanensu.

Da aka yi zaben 2019, akwai mutum 84,004,084 masu katin zabe, kusan daya bisa hudunsu sun fito ne daga Arewa maso yamma mai mutum 20,158,100.

Kara karanta wannan

El-Rufai, Zulum, Gwamnoni 10 da suka Bada Hutun Musamman Domin Yin katin zabe

Na biyu a lissafi su ne Kudu maso yamma (16,292,212), sai Arewa maso tsakiya (13,366,070). 15% na masu rajista suna Kudu maso Kudu (12,841,279).

Yankin Arewa maso gabas da Kudu maso gabas suke da mafi karancin masu kada kuri’a; yankunan suna da mutane 11,289,293 da 10,057,130 a zaben 2019.

Yadda ake ciki a yau

Yanzu maganar da ake yi, babu jihar da aka samu sababbin rajistar masu zabe irin Legas inda ake da karin mutane 508,936 da za su iya yin zabe a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Katin zabe
Ana rajistar katin zabe a Neja Hoto: @INEC Nigeria
Asali: Twitter

Jihohin Kano, Delta, Ribas, Kaduna da Bayelsa sune suka zo na biyu zuwa na shida a rajistar. A Kano mai mutane kusan miliyan 15, an samu karin 500,207.

Har zuwa jiya, alkaluma sun nuna akwai karin mutum 481,929 da suka yi rajista a Delta, Jihar ce ta uku ko da mutanenta ba su wuce miliyan biyar ba.

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

An yi wa Arewa nisa

Katsina mai mutum miliyan 9.3 ta samu karin mutane 283,470 da suka iya kammala rajistar katin zabe. Kusan haka lamarin yake a jihohin Neja da Sokoto.

Hukumar NBS ta ce mutanen da ke rayuwa a Neja da Sokoto sun haura miliyan 12, amma karin da aka samu a rajistar zabensu bai wuce mutum 620, 000 ba.

Duk yawan mutanen Kaduna, jihar na bayan Ribas a wajen rajistar katin zabe. Bayelsa mai mutum miliyan biyu, ta sha gaban su jihohin Filato da Adamawa.

Takaran APC a 2023

A baya kun samu labari hankalin wasu Kiristoci ya tashi a dalilin dauko Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben da za ayi a 2023.

Shugabannin CAN sun zauna da Shugaban Gwamnonin Najeriya, Dr. Kayode Fayemi wanda ya nunawa Kungiyar CAN dalilin zakulo Musulmi daga yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Yansanda Sun Kama Barayi Da Shanu Sama Da 400 A Jihar Gombe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng