Wasu na yunkurin bata mana suna a Najeriya – Shugaba Buhari
- Ministan labarai yace Gwamnatin Buhari ta samu gagarumar nasara
- Lai Mohammed yace sun samu nasara a fannin tattali da yaki da barna
- Alhaji Mohammed yace an kuma samu cigaba a fannin noma da lantarki
Ministan yada labarai na kasar nan Lai Mohammed ya bayyana yadda wasu ke kokarin batawa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari suna da karfi da yaji. Ministan kasar yace wadannan bata-gari na kokarin nunawa jama’a abin da ba haka ba.
Kamar yadda labarin ya zo mana daga Daily Nigerian, Lai Mohammed yace ‘Yan Najeriya su kwantar da hankalin su domin Shugaba Buhari na rike kasar cikin amana. A cewar Ministan an yi nasara a fannin tattalin arziki da yaki da rashawa da tsaro.
KU KARANTA: Ya kamata Shugaba Buhari yayi koyi da 'Yaradua
Lai Mohammed ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da wasu jakadun Najeriya a kasar Sifen. Ministan ya ke fada a Madrid cewa babu wani halin dar-dar da ake fama da shi yanzu a Najeriya illa gyara kasar da Shugaba Buhari ke yi bayan barnar da aka yi.
Gwamnatin Buhari ta nemi a duba irin kokarin da tayi daga hawan ta mulki. Alhaji Lai yace a baya Gwamnatin kasar ta gaza biyan albashin ma’aikata da fansho da kudin ‘yan kwangila. Ministan yace an samu nasara a fannin noma da kuma harkar wutan lantarki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng