Rashin Tsaro: Akwai Yiwuwar A Sace Buhari, In Ji Buba Galadima
- Injiniya Buba Galadima, tsohon na hannun daman Shuagba Muhammadu Buhari ya ce ba abin mamaki bane yan bindiga su iya sace shugaban kasan na Najeriya
- Galadima ya furta hakan ne yayin tsokaci kan halin rashin tsaro da Najeriya ke ciki a baya-bayan nan yana mai cewa yan bindiga sun raina gwamnatin Buhari don sun gane ba za ta iya komai ba
- A cewarsa, da farko an zaci Buhari jarumi ne amma daga bisani aka gano cewa rago ne shi yasa aka cigaba da satar kudin al'umma a kasar kuma ya kasa hana wa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya ce duba da yadda rashin tsaro ke cigaba da tabarbarewa, ba abin mamaki bane a sace shugaban kasar, rahoton Daily Trust.
Galadima ya furta hakan ne yayin martani kan rashin tsaro da ke adabar kasar yayin hira da BBC Hausa ta yi da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Wannan yan bindigan ba su ganin girman gwamnatin Buhari. A farkon gwamnatin, kowa na tsoron shi (Buhari); ana tsamanin zai yi jarumta amma yanzu an gane ba zai iya komai ba.
"Buhari bai san komai ba, ba zai iya komai ba, shi yasa ka ke ganin jami'an gwamnati na sace miliyoyi daga dukiyar talakawa kuma babu wanda ke taka musu birki."
Galadima ya kara da cewa idan yan ta'addan za su iya kutsa wa gidan yarin Kuje, shi kansa shugaban kasa bai tsira ba.
Ya ce:
"Idan ba a dauki mataki ba, yanzu ko nan gaba shima Buhari za a iya sace shi duba da yadda ake watsi da harkar tsaro.
"Zabin kawai da ya rage shine a cigaba da addu'a ko kuma mu mallaki makamai mu kare kanmu amma idan muka dogara ga wannan gwamnantin, tabbas za a kashe mu."
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar
A wani rahoton, fadar shugaban kasa ta yi martani kan bidiyon da yan ta'adda suka fitar na barazanar cewa za su tarwatsa Najeriya, tana cewa jami'an tsaro ba su 'gaza ba kuma basira bata kare musu ba', rahoton Daily Trust.
Yan ta'addan sun fitar da bidiyo inda suka yi barazanar cewa za su sace Shugaba Muhammadu Buhari.
Da ya ke martani, babban hadimin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa shugaban kasa ya yi dukkan abin da ya dace ya yi a matsayinsa na babban kwamandan tsaro ta hanyar karfafa musu gwiwa, siyan kayan aiki da makamai kuma yana tsammanin sakamako mai kyau.
Asali: Legit.ng