Hari kan sojojin fadar Buhari: Runduna ta tabbatar da asarar jami'ai 3, ta musanta sace sojoji

Hari kan sojojin fadar Buhari: Runduna ta tabbatar da asarar jami'ai 3, ta musanta sace sojoji

  • Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar harin da 'yan bindiga suka kai kan jami'an sojin fadar shugaban kasa
  • A karshen makon jiya ne 'yan ta'adda suka yi barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna El-Rufai
  • Rahotanni masu karo da juna sun yi sabani wajen ruwaito adadin asarar da aka yi a harin, amma rundunar ta fayyace komai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojoji uku a wani hari da wasu da ake kyautata zaton yan bindiga ne suka kai wa Sojojin Bataliya ta 7 a ranar Lahadi a hanyar Kubwa zuwa Bwari a babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da rahotanni masu karo da juna game da hasarar rayuka a harin suka karade kasa, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Captain Godfrey Abakpa, ya ce sojoji uku ne suka mutu a arangamar.

Kara karanta wannan

Rundunar Yansandan Najeriya tace ta Tsaurara Matakan Tsaro A Birnin Abuja

Rundunar soji ta tabbatar da kashe jami'anta, ta kayata sace wasu
Hari kan sojojin fadar Buhari: Runduna ta tabbatar da asarar jami'ai 3, ta musanta sace sojoji | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya karyata rahotannin da ke cewa an sace sojoji ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, inji jaridar Leadership.

Haka kuma bai bayyana sunayen sojojin da aka kashe ba amma an tattaro cewa Captain daya ne da sojoji biyu suka mutu a harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Babu wani soja da aka sace, mun samu asarar rauyuka ne kawai, kuma mun kwashe su."

Harin dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da ‘yan ta’addan suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai a wani faifan bidiyo.

Rahotannin leken asiri sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun yiwa babban birnin tarayya kawanya ne da nufin kai hari a makarantar lauyoyi da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja da wasu cibiyoyin gwamnati.

Abokan karatun daya daga cikin sojojin da aka rasa sun magantu da wakilin Legit.ng Hausa

Kara karanta wannan

Fargabar kai hari fadar Buhari: IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

A zantawar wakilin Legit.ng Hausa da daya daga abokan sojan da aka kashe a Abuja mai suna Jauro ya ce:

"Mun yi karatun tattalin arziki a Abu Zaria tare. Gaskiya wannan gwamnatin ta gaza mana.
"Dole ya mutu a jiya saboda wa'adinsa ya qare a duniya.
"Yanzu 'yan fashi sun hanamu sakewa a Najeriya mun gaji da wannan gwamnatin.
"Amma Alhamdulillah ya rasu shaidi."

Daya kuwa da ya samu ganin gawar jami'in ya bayyana cewa:

"Don Allah duka mu yi hakuri.
"Ni da shehi mun samu damar ganin gawarsa kafin a binne shi. Ba abu ne mai dadi ba ganin Jauro yana kwance ba rai ga harbin bindiga kaca-kaca a jikinsa. Abin ta da hankali ne."

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari

A wani labarin, kasa da sa'o'i 24 da 'yan ta'adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El'Rufai a wani faifan bidiyo, wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka yi wa sojojin na Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya Abuja cikin firgici, rahoton The Nation.

‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon harkokin shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da jami'an sojojin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.