Damunan bana: Sanata Goje na jihar Gombe ya yi rabon taki ga manoma a mazabarsa

Damunan bana: Sanata Goje na jihar Gombe ya yi rabon taki ga manoma a mazabarsa

  • Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ya yi rabon takin zamani a mazabarsa a jiya Litinin
  • A baya tsohon gwamnan na Gombe ya raba babura da keke napep da yawa ga mazauna mazabarsa
  • Muhammadu Danjuma Goje na daga cikin jiga-jigan siyasar jihar Gombe da ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Pantami, Gombe - Dan majalisar da ke wakiltar Combe ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Danjuma Goje a jiya ya fara rabon takin NPK buhu 12,000 wanda kudinsu ya kai N258m ga manoman gundumomi da hakimai a kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba na jihar Gombe.

Yayin rabon tallafin da ya gudana a gidansa dake Gombe, Goje ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da sarakuna da hakimai da masu unguwanni da mata da kungiyoyin matasa da kuma manoma a mazabarsa.

Kara karanta wannan

Yansanda Sun Kama Barayi Da Shanu Sama Da 400 A Jihar Gombe

Sanatan Gombe ya rabawa 'yan mazabarsa taki
Damunan bana: Sanata Goje na jihar Gombe ya yi rabon taki ga manoma a mazabarsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wadanda za a rabawa takin

A cewarsa, hakimai 74 a shiyyar ta Gombe ta tsakiya za su karbi buhu uku-uku, inda ya ce masu unguwanni 254 za su samu buhu biyu kowannensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce akwai hakimai 2,537 a mazabar ta majalisar dattawa kuma kowannen su za a ba shi buhun taki daya.

A cewarsa:

“An sayi tireloli 20 na taki jimlar buhu 12,000. Za a rarraba su a mazabar mu. Wannan karimcin na da nufin kawo musu dauki, musamman a wannan lokacin damina da farashin kaya ya yi tsada.
“Muradinmu shi ne mu karfafa wa al’ummarmu ta fuskar tattalin arziki. A ‘yan kwanakin nan, mun baiwa matasan mu tallafin keke napep 1,000 da babura masu yawa kyauta domin yin kasuwanci. An yi hakan ne domin a taimaka musu su zama masu dogaro da kai.”

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya raba tsabar kuɗi miliyan N172m da abinci ga talakawa 30,436 a karamar hukuma ɗaya

Goje ya ja hankalin wadanda suka amfana da rabon da su tabbatar da cewa sun yi amfani da takin domin inganta samar da abinci a jihar da kuma kasa baki daya.

A cewarsa, akwai bukatar a karfafa wa mutane musamman manoma kwarin gwiwar samar da abinci mai yawa domin rage wahalhalun tattalin arzikin da dama ke ciki a yanzu.

Ya kara da cewa, a lokacin da kasar nan ta dogara da kanta a fannin samar da abinci, za a samu raguwar tsananin tashin farashin kayayyaki da koma bayan tattalin arziki.

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya zanta da daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar rabon; Buba Adamu Hassan, wanda ya bayyana jin dadinsa da karamcin Goje.

A cewarsa:

"Ina daya daga cikin wadanda za su dauki takin, kuma ba wannan ne karon farko da zan samu wani abu ta dalilin Goje ba.
"Da na ya samu mashin, ni kuma yau na samu taki, to ni da Goje sai godiya kawai."

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Namune Bamu Da Matsala Dashi - Gwamnonin APC

Abubakar Hassan, wani daban da ya halarci taron ya shaidawa wakilinmu cewa, shi dai ba ya cikin jadawalin masu karbar takin, amma ya bayyana jin dadinsa ganin cewa yakan samu alheri daga sanatan.

A kalamansa:

"Ban samu taki ba amma na samu abin da yafi taki a hannun Goje. Don haka ina taya wadanda suka samu murna, kuma Allah yasa su yi amfani da abin da suka samu ta hanyar da ya dace."

Shirin 2023: Sanatan APC Goje ya raba babura 1000 da keke NAPEP 500 watanni kafin zabe

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje ya fara rabon babura masu kafa uku (Keke Napep) 500 da babura 1000 a mazabarsa a gundumar Gombe ta tsakiya.

A cewar Goje, hakan na daga cikin kokarinsa na yaki da talauci tare da karfafawa talakawan mazabar sa da samar musu da aikin yi, kamar yadda Legit.ng ta samo.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Sanatan na jam’iyyar APC, ya kuma bayyana cewa ya dauki matakin ne domin samar da ayyukan yi ga matasa a yankinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.