Bidiyon Yadda Wani Jami’in Tsaro Balarabe Ke Zuba Hausa Kamar Jakin-Kano A Saudiyya

Bidiyon Yadda Wani Jami’in Tsaro Balarabe Ke Zuba Hausa Kamar Jakin-Kano A Saudiyya

  • An jiyo jami'in tsaron na Saudiya wanda ya kasance Balarabe yana magana da harshen Hausa tiryan-tiryan kamar wani Bahaushen usuli
  • Ahmad wanda yace sunansa na Najeriya 'manya-manya maganin kanana' ya ce Allah ne ya nufa zai ji harshen na Hausa
  • Wannan al'amari ya burge mutane da dama inda suka ce ya yi kokari, wasu kuma sun ce ya yi kamar Bakano

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jama’a sun cika da mamaki bayan bayyana bidiyon wani jami’in dan sandan kasar Saudiyya kuma Balarabe yana Hausa tiryan-tiryan kamar wani Bakano.

A cikin bidiyon wanda shafin _garkuwanarewa ya wallafa a Instagram, an jiwo wani Bahaushe yana yi masa tambayoyi kan yadda aka yi ya iya Hausa haka.

Sai dai kuma, Balaraben wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ahmad ya ce mahaifiyarsa ta haife sa ne a cikin Hausawa.

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

Balarabe
Bidiyon Yadda Wani Jami’in Tsaro Balarabe Ke Zuba Hausa Kamar Jakin-Kano A Saudiyya Hoto: _garkuwanarewa
Asali: Instagram

Ya kuma bayyana cewa sunansa na Najeriya ‘Manya Manya maganin kanana’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai mutumin ya so ci gaba da yi masa tambayoyi inda ya bayyana cewa aiki sun yi masa yawa sosai bai da lokacin amsawa.

Ga yadda hirar tasu ta kaya

Bahaushen ya tambaye shi yaya sunan sa sai Balaraben yace:

“Sunana na nan ko na Najeriya? Sunana na Najeriya ‘manya manya maganin kanana’ amma sunana na nan Ahmad."

Sai Bahaushen ya tambaye shi yaya aka yi ka ji Hausa, sai ya amsa masa da:

“Ka tambayi Allah, domin Allah ne ya bani. Mamata ta haife ni cikin mutanenku."

Da aka tambaye shi a wani unguwa yake sai yace:

“Na nan ko na Najeriya. Na nan Makkah.”

Kalli cikakken bidiyon a kasa:

Martanin mutane kan bidiyon

comrade_bbs1 ya yi martani:

"MashAllah."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Buhari ka ci amanarmu, ko zuciyar Fir'auna gareka sai haka, Malam Bello Yabo

thefarouuq ya ce:

"Kuma hausar tashi kamar Bakano ❤️"

afrahs_collections ta ce:

"Yace aiki ya bani yawagadkiya yayi kokari fa"

Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo

A wani labarin, wata matashiya ta koka a shafin soshiyal midiya bayan ta dawo gida daga Turai ta tarar da danta cikin wani yanayi mara kyan gani.

Da take wallafa bidiyon yaron a shafinta na TikTok mai suna @.its_me_honey, matashiyar ta rubuta cewa tana aiki tukuru a kasar waje.

Ta kara da cewar ta tura dukka kudadenta gida don a kula mata da yaron yadda ya kamata, don haka yanayin da ta riske shi ya raunana mata zuciya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng