Tashin hankali yayin da FGC Kwali ta umurci iyaye su kwashe 'ya'yansu saboda tsoron harin 'yan bindiga

Tashin hankali yayin da FGC Kwali ta umurci iyaye su kwashe 'ya'yansu saboda tsoron harin 'yan bindiga

  • An samu hargitsi a babban birnin tarayya Abuja yayin da hukumar makaranta ta umarci iyaye su kwashe 'ya'yansu
  • An kai hari wani kauye da ke kusa da makarantar, lamarin da ya kai sace wani mutum bayan tafka barna a yankin
  • Iyaye sun tofa albarkacin bakinsu game da rufe makarantar a daidai lokacin da dalibai ke gudanar da jarrabawar zango na uku

Hukumomin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwali, Abuja, sun bukaci iyaye da su kwashe 'ya'yansu daga makarantar saboda fargabar harin da ‘yan ta’adda za su kawo.

Hakan ya haifar da firgici a tsakanin mahukunta da ma'aikata da dalibai da iyayen makarantar, kamar yaddda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Yadda iyaye suka kwashe 'ya'yansu a kwalejin Kwali saboda tsoron 'yan bindiga
Tashin hankali yayin da FGC Kwali ta umurci iyaye su kwashe 'ya'yansu saboda tsoron harin 'yan bindiga | Hoto: GettyImages/Thomas Imo
Asali: Getty Images

Hukumar kula da makarantar ta bukaci iyayen ne da su kwashe ya'yansu sakamakon harin da aka kai a wani kauye da ke kusa, wanda ke da shinge da makarantar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Fargaba Da Tsoro Ya Sa Iyaye Sun Kwashe Yayansu Daga Makaranta A Abuja Bayan Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Da ke Kusa Da Su

Daliban da aka tsara za su kammala jarrabawar zango na uku a ranar Talata, tuni aka tura su gidan iyayensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mahaifi daya kwashi 'ya'yansa, ya kuma bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar cewa makarantar ce ta tuntubi iyayen game da wannan batu.

A cewarsa:

"Na dauko su ne daga magamar Giri. Malamin da ke kula dasu ne ya kira ya sanar da mu.
“A halin yanzu, jarrabawar tana ci gaba da gudana. Wasu dalibai har yanzu suna makale a can, suna jiran iyayensu.”

Dalilin umarnin a kwashe dalibai daga makarantar

Shugaban kungiyar iyaye da malamai (PTA) na makarantar, Suleiman Idajili, a wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar ta Premium Times, ya ce umarnin ya biyo bayan harin da aka kai a wani kauye ne da ke kusa da makarantar da safiyar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Ya ce ‘yan ta’adda sun kai hari kauyen da ke da shinge da makarantar inda suka yi awon gaba da wani mutum da matarsa. Ya ce daga baya ‘yan ta’addan sun tafi da mijin suka bar matar.

Ya kara da cewa matakin gaggawa da jami’an tsaro a makarantar suka yi ne ya kare ta daga barnar ‘yan ta’addan.

Ya ce hukumar makarantar ta umurci iyayen yara da su kwashe 'ya'yansu nan da zuwa ranar Litinin, amma wadanda ke kusa da makarantar sun zabi su kwashe yaran nasu a ranar ta Lahadi.

Ya ce matakin ya samu amincewar jami’an ma’aikatar ilimi ta tarayya wadanda ya bayyana cewa sun ziyarci makarantar tun a ranar Lahadi.

Ya ce:

“A hukumance, mun ce su zo gobe (Litinin). Amma wadanda ke kusa suka zo suka kwashe 'ya'yansu a yau. Kuma da yawa daga cikinsu sun zo yau.”
“Saboda daukin gaggawar da sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da ke harabar makarantar suka yi ne ya sa su (’yan ta’adda) ba su shiga harabar makarantar ba.

Kara karanta wannan

Matashi ya caccaki 'yan mata, ya ce duk budurwar da bata tashi bacci har 8, to malalaciya ce

"Don haka, shi ya sa ya zama mana dole mu dauki mataki saboda ba mu san shirinsu na gaba ba."

Kokarin yin magana da Daraktan Yada Labarai a ma’aikatar ilimi, Ben Goong, bai samu ba a ranar Lahadin da ta gabata, saboda bai dauki kiran waya ba.

Shugaban PTA ya kawar da tsoron da ke zukatan iyaye

A halin da ake ciki, Mista Idajili ya tabbatar wa iyaye cewa jami’an tsaro suna nan a kasa domin su dakile duk wani kutse daga maharan.

Yace:

“Muna da tsauraran matakan tsaro don tabbatar da tsaron wadanda iyayensu ba su zo sun dauke su da daren nan ba. Sojojin na nan a kasa. ‘Yan sanda suna nan; ‘yan sandan sirri da ‘yan banga duk sun shiga lamarin.”

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Adeh Josephine, ta ce ba ta da masaniya kan faruwar lamarin.

Ta yi alkawarin cewa za ta yi bincike kuma ta ba da bayanai daga baya. Sai dai har yanzu ba ta yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Kannywood: Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

Jami’in ’yan sandan shiyya (DPO) na reshen Kwali, bai amsa kiran wayan da jaridar ta yi masa ba.

Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama

A wani labarin, majiyoyin tsaro, a ranar Laraba, sun bayyana cewa sojojin da aka tura yankin Kuje da kewayen magarkama, wadanda suka yiwa yankin farin sani, an sauya musu mazauni sa’o’i 24 kafin ‘yan ta’adda su kai hari gidan yarin Kuje.

Majiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa aka kwashe su jami'an da suka san yankin sa'o'i 24 kafin harin, kuma har yanzu ba a samun wasu da suka maye gurbinsu ba har 'yan ta'addar suka far wa yankin, inji Vanguard.

Sai dai kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wa'adin da ya kamata sojojin su zauna a wannan yankin ya wuce kuma dama ya kamata a sauya su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.