Dirama yayin da 'yan fashi suka dura coci ana tsaka da bautar ranar Lahadi, suka yiwa fasto da mabiyansa fashi

Dirama yayin da 'yan fashi suka dura coci ana tsaka da bautar ranar Lahadi, suka yiwa fasto da mabiyansa fashi

  • Wani faifan bidiyo ya nuna lokacin da wasu ’yan fashi da makami suka dura kan wani fasto ana tsakiyar hidimar bauta ta ranar Lahadi
  • 'Yan fashin sun tilasta faston mai suna Whitehead ya kwanta a kasa yayin da suke bin mutanen da ke cikin cocin suna kwace musu abubuwa
  • Rahotanni sun ce barayin sun kwashi kayan ado na akalla KSh miliyan 47 daga Whitehead, matarsa da kuma wadanda ke cikin cocin

An yi wa wani babban fasto na Brooklyn fashi a lokacin hidimar bauta da aka yi ta kai tsaye a ranar Lahadi, 24 ga Yuli.

Kamar yadda aka gani a cikin wani faifan bidiyo, faston ya ga shigowar wasu tsageru rike da bindiga cocinsa a lokacin da yake kan mimbari yana kwada wa'azin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Shari'a: Mutane 3 da suka rayu a magarkama na tsawon shekarau, aka gano ba su da laifi

Jaridar New York Post ta ruwaito cewa tsagerun sun tafi da kayan ado na karafa masu daraja da suka kai KSh miliyan 47, a cewar masu bincike.

Yadda aka yiwa fasto fashi a cikin cocinsa
Dirama yayin da 'yan fashi suka dura coci ana tsaka da bautar ranar Lahadi, suka yiwa fasto da mabiyansa fashi | Hoto: No Jumper
Asali: UGC

Whitehead yana tsakiyar wa'azinsa ne a Cibiyar Leaders of Tomorrow International a Canarsie lokacin da yan bindigar da ke rufe da fuska su uku suka kutsa kai suka yi barnarsu, in ji 'yan sanda.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Whitehead ya tambayi mabiyansa, kafin ya hango 'yan fashin dauke da makamai cewa:

"Nawa ne a cikinku kuka rasa imaninku saboda kun ga wani ya mutu?"

Da nan sai 'yan bindigan suka shigo, suka fara aiwatar da barnar da ta kawo su ta yin fashi da kwace kayan jama a.

Kalli bidiyon:

Tashin hankali yayin da FGC Kwali ta umurci iyaye su kwashe 'ya'yansu saboda tsoron harin 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

A wani labarin, Hukumomin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwali, Abuja, sun bukaci iyaye da su kwashe 'ya'yansu daga makarantar saboda fargabar harin da ‘yan ta’adda za su kawo.

Hakan ya haifar da firgici a tsakanin mahukunta da ma'aikata da dalibai da iyayen makarantar, kamar yaddda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar kula da makarantar ta bukaci iyayen ne da su kwashe ya'yansu sakamakon harin da aka kai a wani kauye da ke kusa, wanda ke da shinge da makarantar. Wani mahaifi da kwashi 'ya'yansa, ya kuma bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar cewa makarantar ce ta tuntubi iyayen game da wannan batu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.