Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a

Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a

  • Bayan cin karo da bidiyon ta, gidauniyar Bashir Ahmad ta bayar da tallafin karatu ga yar Kano mai baiwar lissafi
  • Tsohon hadimin shugaban kasa ya yi tattaki har inda iyayen Saratu Dan-Azumi suke domin neman yardarsu kan su amince su dauki nauyin karatunta
  • Yanzu dai Saratu za ta yi karatu kyauta tun daga Firamare har zuwa matakin jami'a sannan wani sanata ya dauki nauyin bayar da babur din kaita da daukota daga makaranta

Allah ya tarbawa garin wata karamar yarinya yar asalin jihar Kano nono, inda ta samu tallafin karatu kyauta tun daga Firamare har zuwa jami’a.

Saratu Dan-Azumi kamar yadda aka bayyana sunanta, ta kasance hazikar yarinya wacce Allah ya yiwa baiwar hada lissafi duk da karancin shekarunta.

Saratu da Bashir
Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a Hoto: @BashirFund
Asali: Twitter

Gidauniyar tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ne ya dauki nauyin karatun Saratu bayan ya samu yardar mahaifanta.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Ahmad ya bazama neman yarinyar da iyayenta ne tun bayan da ya ci karo da bidiyonta wanda ke ta yawo a shafukan soshiyal midiya inda ake mata tambayoyi masu zurfi a bangaren lissafi kuma tana bayar da amsa daidai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon hadimin shugaban kasar ne ya sanar da batun tallafin da gidauniyarsa ta baiwa yarinyar a shafin Twitter.

Gidauniyar ta rubuta:

“Mun gode da wannan bidiyo. Mun ziyarci danginta a yau. Alhamdulillah, sun yarda da bukatarmu na daukar nauyin karatun yarinyar tun daga Firamare har zuwa Jami’a. Nan take za a yi mata rijista a makarantar firamare ta NYSC, Gaya sannan daga bisani za ta shiga sabuwar cibiyar fasaha ta Gaya.”

An dauki nauyin kula da jin dadin iyayenta

Hakazalika, wani mai amfani da shafin Facbook, Tahir Mahmood Saleh ya ce sun yi tattaki har zuwa karamar hukumar Gaya bayan cin karo da bidiyon domin a cewarsa mutane da dama sun nuna sha’awar tallafawa yarinyar.

Kara karanta wannan

Bidiyon magidanci da kanwar matarsa a bandaki, yayi alkawarin siya mata iPhone idan ta kwanta da shi

Saleh ya ce sun kai ziyarar ne a madadin Dr. Musa Abdullahi Sufi da gidauniyar Farfesa Abubakar Gwarzo ta dauki bangaren tallafawa iyayen yarinyar domin samar da jin dadi mai dorewa.

Har ila yau, ya kuma yace akwai wani daga cikin sanatoci da yace zai bayar da babur ga dan uwan yarinyar wanda za a dinga kai ta da daukko ta daga makaranta.

Legit Hausa ta tuntubi Mallam Saleh don jin karin bayani daga wajensa kan batun tallafin da za a baiwa iyayen yarinyar inda ya jaddada cewa gidauniyar Gwarzo za ta basu jari.

Ya ce:

“Su Gwarzo Foundation suna shirin baiwa iyayenta jari ne domin suyi kasuwanci. Sun baiwa iyayen dama su fitar da Sana’ar da suke so domin Gidauniyar su ta basu jari sannan kuma zasu kafa wani kasuwanci na daban ga Saratu wanda wannan nata ne na gashin kanta.”

Matar Da Ta Haifi Yara 44 Ta Ce Tana Son Kari, Likitoci Sun Kasa Juya Mahaifarta

Kara karanta wannan

Kannywood: Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labarin, wata mata a kasar Uganda ta hau kanen labarai kan samun abun da ba dukka mata ke mallaka ba, musamman a shekarunta.

Mariam Nabatanzi ta kasance mace mai shekaru 41 a duniya wacce ke da yara 44 a gabanta kuma ita kadai ke kula da su. Uwar Uganda ko uwar Afrika kamar yadda ake kiranta, Natabanzi ta bayyana cewa ba za ta daina haihuwar ‘ya’ya ba.

Nabatanzi ta ce ta haifi dukka yaranta ne a yayin soyayya da wani mutum, wanda ya yi watsi da ita, kamar yadda Afrimax English ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng