Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun Sace Mutune 50 A Jihar Neja

Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun Sace Mutune 50 A Jihar Neja

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari a kauyen Kuchi da ke karamar hukumar Munya na Jihar Neja a daren ranar Juma'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun rika bi gida gida suna kwasar mutane inda daga karshe tattara mutane a kalla guda 50 suka tafi da su
  • Emmanuel Umar, kwamishinan tsaron cikin gida da jin kan mutane ya tabbatar da sace mutanen amma ya ce ba zai iya tabbatar da adadin ba kuma sun sanar da yan sanda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Neja - Yan ta'adda sun sace mutane hamsin daga garin Kuchi, a karamar hukumar Munya na Jihar Neja, The Punch ta rahoto.

A cewar shugaban kungiyar matasan Shiroro a Jihar Neja, Sani Kokki, wanda ya bayyana hakan cikin sanarwar da ta bawa The Punch, ya ce an sace mutanen ne misalin karfe 2 na dare yayin da ake ruwan sama.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, Mun ba Shugaban Kasa Rahoton Fasa Gidan Yarin Kuje inji Minista

Taswirar Jihar Neja
Tashin Hankali: Yan Ta'adda Sun Sace Mutum 50 a Jihar Neja. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Rahotanni da aka tabbatar ya nuna yan ta'adda da yawa sun kai hari a garin cikin dare inda suka sace mutane da yawa," in ji Kokki.

Ya ce yan ta'addan sun bi gida-gida suka rika daukan mutane lokacin ana ruwan sama.

"Sun kutsa garin misalin karfe 2 na dare yayin da ake ruwa, nan take suka fara bi gida-gida suka tattara mutane suka tafi da su mabuyarsu," in ji sanarwar.

Ya kara da cewa babu wanda aka ce, ya kuma ce adadin mutanen da aka sace guda 50 ne.

"Duk da cewa a yanzu babu wani rahoton mutuwa, an kayyade adadin mutanen aka sace ya kai 50," in ji Kokki.

Kokki ya kuma ce yan ta'addan da wadanda suka sace sun gaza tsallaka rafi saboda ruwan sama da ya yi yawa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano

"Sai dai, rahotanni sun ce yan ta'addan da wadanda suka sace sun gaza cigaba da tafiyarsu saboda ruwa da ya cika ya batse daga Rafin Dangunu ya rufe hanya."

Da aka tuntube shi, kwamishinan tsaron cikin gida da jin kan mutane, Emmanuel Umar, ya tabbatar da sace mutanen, ya kara da cewa an sanar da jami'an tsaro.

"Jami'an tsaro sun amsa kira tun karfe 5 na safe kuma muna sauraron rahoto daga gare su," in ji shi.

Da aka tambaye shi adadin mutanen da aka sace, Umar ya ce bai da tabbas saboda mutane da dama sun tsere.

"Ba zan iya tabbatar da adadin wadanda aka sace ba domin a yanzu yan kauyen da yawa sun tsere kuma sai sun dawo kafin mu san adadin mutanen da aka sace," in ji Umar.

'Yan Bindiga Sun Bindige 'Yan Sandan Sintiri 5 a Katsina

A wani rahoton, yan bindiga sun kashe yan sandan sintiri biyar da fararen hula uku a garin Gatikawa, karamar hukumar Kankara a Katsina.

Kara karanta wannan

2023: Ku Dena Yin Sojan Gona Da Sunan Mu, CAN Ta Gargadi Yan Siyasan Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa yan sandan sun taho daga Kano ne domin yin wani aiki na musamman, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel