'Yan Bindiga Sun Bindige 'Yan Sandan Sintiri 5 a Katsina

'Yan Bindiga Sun Bindige 'Yan Sandan Sintiri 5 a Katsina

  • Jami'an yan sandan Najeriya guda biyar da fararen hula uku sun riga mu gidan gaskiya sakamakon bindige su da yan bindiga suka yi a Katsina
  • Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da yamma misalin karfe 5.35 lokacin da yan bindigan a kan babura suka kawo hari a Gatikawa
  • Yan bindigan sun kuma dauki lokaci suka rika shiga gida-gida suna yi wa mutane kwacen abubuwa masu muhimmanci da kudi da kayan abinci da sauransu

Jihar Katsina - Yan bindiga sun kashe yan sandan sintiri biyar da fararen hula uku a garin Gatikawa, karamar hukumar Kankara a Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa yan sandan sun taho daga Kano ne domin yin wani aiki na musamman, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali, 'yan bindiga sun farmaki mazauna a jihar Neja

Yan Bindiga
'Yan Bindiga Sun Bindige 'Yan Sandan Sintiri 5 a Katsina. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne misalin karfe 5.35 na yammacin ranar Laraba, lokacin da fiye da yan bindiga 300 suka kai hari garin suka fara harbe-harbe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daya daga cikin majiyoyi ya ce yan bindigan, wadanda suka taho da manyan bindigu kan babura, sun rika bi gida-gida suna kwace duk wani abu mai muhimmanci, har da kudi da kayan abinci.

Ya ce an raunata mutanen jihar da dama, musamman wadanda suka yi yunkurin su gudu.

Ya ce mutane sun firgita bayan harin, wasu ma sun tsere zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su don tsoron kada a sake kawo harin.

Wannan shine karo na biyu a cikin wata guda da yan bindiga ke kashe yan sanda.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah bai daga wayarsa ba da wakilin Daily Trust ya kira shi domin jin ba'asi game da lamarin.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, In Ji Rundunar Yan Sanda

A wani rahoton, rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa shugaban yan bindiga, Ado Aleru, wanda aka nada sarauta ranar Alhamis da ta gabata a masarautar Yandoto Daji a Zamfara, har yanzu suna nemansa ruwa a jallo.

Rundunar yan sandan ta ce ana zargin Alero da kashe mutane 100 mazauna Jihar Katsina, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kakakin rundunar, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke martani kan nadin sarautar da aka yi wa shugaban yan bindigan a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel