Bidiyon tsohon gwamna da matarsa suna cin duniya da tsinke a wata fitar dare da suka yi
- Bidiyon tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, tare da matarsa Ebele a wata fitar dare da suka yi ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani
- A bidiyon da rahotanni suka ce an dauke shi a Jamhuriyar Dominican ne, an ga gwamnan da matarsa suna cashewa tare da rakashewa cike da nishadi
- Bidiyon na nuna wani wuri inda suka ziyarta da dare kuma an yi shigar fararen kaya ana cin duniya da tsinke cike da annashuwa da nishadi
Bidiyon tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano tare da matarsa Ebele suna shakatawa tare da shagali a kasar waje ya yadu.
Rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce an dauka bidiyon ne a Jamhuriyar Dominican inda tsohon gwamnan jihar Anambra ya je hutu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A bidiyon wanda gajere ne, an ga gwamnan da matarsa suna chashewa tare da shakatawa a wani taro wanda duk an saka fararen kaya.
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta damke Obiano a watan Maris jim kadan bayan ya mika madafun iko ga sabon gwamnan jihar, Charles Soludo.
An damke tsohon gwamnan saboda zarginsa da ake yi da waddaka tare da rub da ciki kan makuden kudade har N5 biliyan da N37 biliyan wanda ya cire su daga asusun jihar.
Bayan kwashe kwanaki bakwai a magarkamar hukumar EFCC, sun sake shi bayan an nemi belinsa.
Kalla bidiyon gwamnan da matarsa:
Bidiyon tsohon gwamna yana shan ruwa cike da damuwa a ofishin EFCC
A wani labari na daban, mai rajin kare hakkin da Adam, Deji Adeyanju, ya wallafa wani bidiyo na tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya na shan ruwan gora yayin da ya ke ofishin hukumar yaki da rashawa tare hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Idan za a tuna, an yi ram da tsohon gwamnan jihar Anambran a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas yayin da yake kokarin tafiya Houston, Ingila.
Wannan kamen ya zo ne sa'o'i kadan bbayan gwamnan kudu maso gabas din ya mika mulki ga sabon gwamna Charles Soludo.
Asali: Legit.ng