Akalla Mutane 30 Sun Mutu, Motoci 3 Sun Kone a Mummunan Hadarin Motan Kaduna
- An samu mummunan hadarin mota a hanyar Zaria zuwa Kano a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Akalla mutane 30 ne suka mutu, kana an kwashe wasu da dama da suka ji raunuka zuwa asibitin da ke kusa
- Majiyoyi sun bayyana yadda lamarin ya faru, sun kuma ta'allaka laifin hadarin ga tsananin gudun da motocin ke yi
Makarfi, Kaduna - Akalla mutane 30 ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Zaria zuwa Kano ranar Alhamis 21 ga watan Yuli.
Hadarin ya auku ne da misalin karfe 5:30 na yamma a kusa da Hawan Mai Mashi da ke karamar hukumar Makarfi a jihar Kaduna.
Abdurahman Yakasai, mataimakin kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya mai kula da shiyyar Zaria, ya tabbatar wa da Daily Trust faruwar hatsarin.
Ya ce hatsarin motan ya hada ne da motocin bas kirar Toyota mai daukar mutum 18 guda biyu da kuma kirar Gulf, inda ya kara da cewa hadarin ya faru ne sakamakon tsananin gudun motocin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Wadanda suka samu raunukan an garzaya da su asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da Shika a Zaria, yayin da sauran wadanda suka mutun kuma aka kwashe su aka ajiye su a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin."
Kwamandan sashin ya ce hukumar ta FRSC har yanzu ba ta tantance adadin motocin ba saboda sun kone kurmus.
Sai dai ya ce ana kokarin samun bayanai da cikakkun bayanai na wadanda abin ya shafa.
A bangare guda, wani ganau mai suna Suleiman Mohammed ya shaida wa jaridar cewa, saboda tsananin wutar da ta kama motocin uku, da kyar mutane suka iya kubutar da wasu daga wadanda abin ya shafa.
Tashin hankali: Sabuwar cuta ta bullo a wata makaranta, mutum 10 sun jikkata, 1 ya mutu
A wani labarin, an kwantar da mutane goma a asibiti kana wani ya mutu daga wata nau'in cuta da ta bulla a Boji-Boa na jihar Delta.
Cutar dai ta dumfari daliban makarantar Mary Mount College ne, inda ta tabbata a jikin mutum biyar. An ce daga alamar ta akwai suma da faduwa haka siddan.
Jaridar Leadership ta bibiyi lamarin a ma'aikatar lafiya ta jihar, inda ta tabbatar da cewa ana kula da mutum hudu da suka rayu a wani asbitin gwamnati da ke jihar.
Asali: Legit.ng