Yan Sanda Sun Sake Kama Wasu Da Suka Tsere Daga Kurkukun Kuje A Jihohin Arewa 2
- Yan sanda sun damke wasu fursunoni biyu da suka tsere sakamakon harin da yan bindiga suka kai magarkamar Kuje
- Abubakar Mohammed wanda ake tuhuma da ta'addanci ya shiga hannu a jihar Adamawa yayin da aka damke Ebube Igwe Jude da ke jiran shari'a a Benue
- Ana ci gaba da kokarin ganin an tattaro kan dukkanin fursunonin da suka arce daga gidan gyara halin
Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum da ya tsere daga gidan yarin Kuje yayin da yake kokarin komawa Bama, mahaifarsa da ke jihar Borno.
Fursunan mai shekaru 23, Abubakar Mohammed, na fuskantar tuhume-tuhume na ta’addanci.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yan sanda, Sikiru Akande, wanda ya ce an kama fursunan ne a iyakar Adamawa/Borno, Daily Trust ta rahoto.
Akande ya kuma bayyana cewa rundunar ta kuma kwato makamai da kama wasu mutane 12 da ake zaton yan fashi da makami ne a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wani lamarin kuma, rundunar yan sanda a jihar Benue a ranar Alhamis ta ce jami’anta sun kama wani Ebube Igwe Jude, wanda ya tsere daga gidan gyara hali na Kuje bayan harin da yan bindiga suka kai kwanaki.
Kakakin rundunar, SP Catherine Anene, a cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa Jami’an da aka tura don su binciki lamarin ne suka kama shi a hanyar George Akume Way, Wurukum a Makurdi, Nigerian Tribune ta rahoto.
Anene ta ce:
“A ranar 19/7/2022, da misalin karfe 3:00 na rana, an samu bayani game da wani Ebube Igwe Jude, wani fursuna da ya isa Makurdi sakamakon harin gidan yarin Kuje.
“A yayin bincike, ya fallasa cewa ya tsere ne daga gidan yarin Kuje a lokacin fashin magarkamar. Ya bayyana cewa fuskantar shari’a ne kan kisan kai da ke da alaka da budurwarsa.
Anene ta kara da cewa rundunar ta fara shirin mika wanda ya tseren a hannun hukumar gyara halin Najeriya don daukar matakin da ya dace.
An Ceto Yan Sanda 10 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kogi
A wani labari na daban, mun ji cewa an yi nasarar ceto jami’an yan sanda 10 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kogi.
An tattaro cewa an ceto jami’an tsaron ne a daren ranar Laraba, 20 ga watan Yuli.
An dai yi garkuwa da yan sandan ne a ranar Lahadi yayin da suke dawowa daga aikin zabe da suka yi a jihar Osun.
Asali: Legit.ng