An Ceto Yan Sanda 10 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kogi

An Ceto Yan Sanda 10 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kogi

  • Jami'an yan sandan da wasu miyagun yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kogi sun kubuta
  • An ceto jami'an yan sandan su 10 a wuraren kauyen Jakura da ke Obajana ta jihar Kogi a ranar Laraba
  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa an kwashi jami'an nata wadanda aka kubutar ba tare da rauni ba zuwa asibitinta da ke Lokoja don basu cikakken kulawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kogi - Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an yi nasarar ceto jami’an yan sanda 10 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kogi.

An tattaro cewa an ceto jami’an tsaron ne a daren ranar Laraba, 20 ga watan Yuli.

An dai yi garkuwa da yan sandan ne a ranar Lahadi yayin da suke dawowa daga aikin zabe da suka yi a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali, 'yan bindiga sun farmaki mazauna a jihar Neja

Yan sanda
An Ceto Yan Sanda 10 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Labarin sakin nasu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumomin yan sandan suka fitar, jaridar Premium Times ta kuma rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

“An ceto dukkanin jami’ai 10 da aka yi garkuwa da su ba tare da rauni ba.”

An ceto su ne a wuraren kauyen Jakura da ke Obajana kuma an dauke su zuwa asibitin yan sanda da ke Lokoja don samun kulawar likitoci.

Miyagun 'Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 10 a jihar Kogi

A baya mun kawo cewa wasu miyagu da ake zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Nasarawa 10 ranar Lahadi a jihar Kogi.

Jami'an yan sandan sun shiga hannun masu garkuwan ne yayin da suke kan hanyar komawa wurin aikin su daga jihar Osun, inda aka tura su ba da tsaro a zaɓen gwamna da aka kammala ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'an yan sanda 10 a jihar arewa

Wata majiya ta shaida wa jaridar Guardian cewa maharan sun yi awon gaba da jami'an yan sandan ne a yankin Obajana da ke jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng