Miyagun 'Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 10 a jihar Kogi

Miyagun 'Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 10 a jihar Kogi

  • A kan hanyarsu ta koma wa wurin aiki daga jihar Osun, wasu yan sanda 10 sun faɗa hannun masu garkuwa da mutane a Kogi
  • Bayanai sun tabbatar da cewa yan sandan sun tsaya gyaran mota a daji, ba zato yan bindiga suka farmake su a Obajana
  • Tuni hukumar yan sanda ta tura jami'an sashin yaƙi da garkuwa domin bibiya da damƙo yan ta'addan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kogi - Wasu miyagu da ake zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Nasarawa 10 ranar Lahadi a jihar Kogi.

Jami'an yan sandan sun shiga hannun masu garkuwan ne yayin da suke kan hanyar komawa wurin aikin su daga jihar Osun, inda aka tura su ba da tsaro a zaɓen gwamna da aka kammala ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari kan ɗalibai a wata Jami'ar Najeriya, sun mamaye Hostel ɗin mata

Yan sanda.
Miyagun 'Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 10 a jihar Kogi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida wa jaridar Guardian cewa maharan sun yi awon gaba da jami'an yan sandan ne a yankin Obajana da ke jihar Kogi.

Majiyar ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A ranar 17 ga watan Yuli, 2022 da misalin ƙarfe 11:05 na safe DPO na Obajana ya samu rahoton cewa an jiyo ƙarar harbin bindiga a hanyar Bye Pass, kusa da Tashar manyan motoci PTI Obajana."
"Nan take DPO ya haɗa tawagar dakarun sintiri suka dira wurin, inda suka ci karo da Motar Bas mai ɗaukar mutum 18 da lambar rijista GWA 295 YR wani mai suna Usman Abdullahi na tuƙa ta ɗauke da fasinja 6 kacal."
"Mutane 7 na cikin motar sun bayyana kansu da jami'ai da ke aiki a hukumar yan sandan Nasarawa kuma suna kan hanyar koma wa wurin aiki ne daga jihar Osun."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

Yadda lamarin ya faru

A ruwayar Premium Times, majiyar ta ƙara da cewa:

"Ragowar na cikin motar sun ba da labarin cewa suna tsaka da tafiya motar ta ɗan samu matsala kuma da suka tsaya don gyarawa ba zato sai ga yan bindiga sun fito daga cikin jeji, suka sace mutum 10."

A halin yanzun an tura dakarun yan sanda na sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane zuwa yankin domin binciko inda yan ta'addan suka yi.

A wani labarin kuma kun ji cewa hadimin gwamnan jihar Nasarawa ya rasu a wani haɗarin mota da ya rutsa da shi

Mai taimakawa gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa kan harkokin wutar lantarki, Jamilu Mohammed Yakubu, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Yakubu ya rasu ne ranar Talata a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Akwanga-Lafia jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Hanyarsa Ta Dawowa Da Gonarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel