Gwamnatin Buhari za ta kashe N6.72trn a matsayin tallafin man fetur a 2023
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta kashe makudan triliyoyi a matsayin kudaden tallafin man fetur a shekara mai zuwa
- A makon nan ne aka samu karin farashin man fetur, lamarin da ya firgita 'yan Najeriya da dama
- Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fafutuka don kawo mafita a harkar da ta shafi man fetur da samuwarsa a kasar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta tanadi kudaden tallafin man fetur a shekarar 2023 da akalla za su kai sama da Naira tiriliyan 6.72.
Ministar Kudi ta Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis yayin taron kashe kudade na 2023 – 2025 na MTEF da FSP, The Nation ta ruwaito.
Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta yi hasashen sakamakon kasafin kudi matsakaici ta fuska da yanayi biyu dangane da ma'auni na kasafin kudin Najeriya.
A yanayin farko, Ministar ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"An kiyasta tallafin man fetur a kan Naira Tiriliyan 6.72 na cikar shekarar 2023".
Wannan adadin ta ce "zai ci gaba da zama kuma NNPC za ta ba da shi gaba daya a madadin kasa".
A yanayi na biyu da ministar ta bayyana shi ne:
"Tallafin man fetur zai kasance har zuwa tsakiyar 2023 bisa la'akari da karin watanni 18 da aka sanar a farkon 2021, inda za a samar da Naira tiriliyan 3.36."
Ministan ya yi gargadin cewa dukkanin yanayin biyu suna da tasiri ga ci gaban tsabar kudade a Asusun Tarayya.
A rahoton da jaridar Vanguard ta kawo, Zainab Ahmed ta kara da cewa:
"Za a kawo tsauraran matakan aiwatar da tsarin gudanar da ayyuka na Kamfanoni Mallakan Gwamnati (GOEs) wanda zai kara yawan rarar kudaden aiki da rarrabawa a 2023".
NNPC ta lallaba tayi karin farashin man fetur a fadin Najeriya, lita ya tashi daga N165
A wani labarin, kamfanin mai na kasa watau NNPC Limited, ya amince da karin farashin litar fetur daga N165 da aka sani a gidajen mai zuwa akalla N179.
Rahoto ya fito daga The Guardian cewa karin da kamfanin NNPC suka yi zai fara aiki daga yau Talata, 19 ga watan Yuli 2022 a gidajen man kasar nan.
NNPC ya sanar da ‘yan kasuwa cewa su canza farashin da suke saidawa mutane litar man fetur. Ana sa ran daga yau sabon farashin zai fara aiki a ko ina.
Asali: Legit.ng