Kwararru: Mutum 6,000 cikin 31,000 ne suka tsallake jarrabawar neman aiki ta Soludo

Kwararru: Mutum 6,000 cikin 31,000 ne suka tsallake jarrabawar neman aiki ta Soludo

  • Gwamnatin jihar Anambra ta bayyana adadin mutanen da suka tsallake jarrabawar daukar ma'aikatan makarantun firamare da sakandare
  • A baya an yi cece-kuce kan jarrabawar da aka yiwa masu neman aiki, inda gwamna ya umarci a soke sakamakon tare da sake jarrabawar
  • Jihohi da dama a Najeriya sun sha yin jarrabawar daukar aiki, kana an sha samun tasgaro yayin da masu neman aikin ke faduwa jarrabawa

Awka, jihar Anambra - Kasa da mutane 6,000 daga cikin 31,000 da suka rubuta jarabawar daukar malamai ta yanar gizo a jihar Anambra suka yi nasara, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan jihar, Farfesa Chukwuma Soludo ya ba da umarnin a dauki malaman makarantun firamare da sakandare aiki a makarantun jihar bayan watanni biyu kacal da hawansa mulki don bunkasa yawan malamai ga dalibai a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Mutum 6000 sun tsallake jarrabawar neman aiki a Anambra
Kwararru: Mutum 6,000 ciki 31,000 ne suka tsallake jarrabawar neman aiki ta Soludo | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Mista Paul Nwosu ne ya bayyana hakan a jiya bayan taron Majalisar Zartarwa na mako-mako na jihar a Awka.

Ya bayyana cewa, biyo bayan jarabawar da malamai suka yi na CBT, an tantance mutum 6,250 domin tattaunawa ta baki-da-baki a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, za a tura 3,250 ga makarantun firamare, yayin da 3,000 za su tafi makarantun sakandare, inda ya ce za a fara tattaunawar ta baki-da-baki ne a ranar 27 ga watan Yuli, 2022, kuma za a dauki tsawon makwanni biyu ana yi.

Nwosu ya ce:

“Tattaunawar da za ta zo ne cikin rukuni-rukuni, za a yi ta ne a Makarantar Grammar ta Igwebuike Awka; St John of God Secondary School, Awka da kuma hukumar ilimi ta bai daya ta jihar Anambra (ASUBEB) da ke Awka.”

A baya kadan, biyo bayan rigimar da ta biyo bayan CBT na farko ta yanar gizo, gwamna Soludo ya bayar da umarnin soke jarrabawar kuma ya bada umarnin a sake ta, inda gwamnatin jihar ta dauki nauyin kudin da masu neman aikin za su kashe a dawainiyar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Rashin da'a: Mataimakan gwamna 5 da aka tsige su a Najeriya, amma kotu ta mayar dasu

Kaduna: Gwamnatin El-Rufai ta sanar da ranar da za ta fara daukar malamai 10,000

A jihar Kaduna kuwa, gwamna Nasir El-Rufai ya amince da tsarin aiki na hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) na daukar malamai 10,000 ta kafar yanar gizo.

Wata sanarwa da Shugaban Hukumar KADSUBEB, Malam Tijjani Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa hukumar ta baiwa Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) aikin kirkira kafar daukar ma’aikata, wadda za ta fara aiki a ranar Alhamis, 21 ga Yuli, 2022.

Hakazalika, sanarwar ta ce masu bukatar cike fom din neman aikin dole ne su zama masu NCE da masu digiri na farko a fannin Ilimi (B.Ed, B.A EED, B.Sc, Bd, B.Tech daga jami'o'in da gwamnati ta amince dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel