Kun cika taurin kai: Gwamnatin Buhari ta caccaki ASUU, ta ce su suka aje dalibai a gida

Kun cika taurin kai: Gwamnatin Buhari ta caccaki ASUU, ta ce su suka aje dalibai a gida

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a shirye take ta kawo karshen yajin ASUU, amma kungiyar ce ke kawo cikas
  • Kungiyar malaman jami'o'i sun shafe sama da watanni hudu suna yajin aiki, lamarin da ya sa dalibai ke zaune a gida
  • Gwamnati ta dage cewa, tana shirye da kawo mafita, kana ta ce saura kiris ta kammala tattaunawa da kungiyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta zo da wani batu, ce za a iya magance matsalolin da suka shafi yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yi idan da masu ruwa da tsaki manyan ASUU ba su yi “taurin kai ba”.

Idan baku manta ba, kungiyar ASUU ta shafe sama da watanni hudu tana yajin aiki saboda wasu bukatu da gwamnatin Najeriya ta gaza biya musu.

Kara karanta wannan

Kano: Dakin Ajiya Da Wasu Wurare Sun Kone Kurmus A Gobarar Da Ta Tashi a Makarantar Yaran Ma'aikatan Jami'ar BUK

Gwamnatin Buhari ta ce ASUU ke jan kafa kan batun yajin aiki
Sun cika taurin kai: Gwamnatin Buhari ta caccaki ASUU, ta ce su suka aje dalibai a gida | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A baya kun ji cewa, a wani taro a jiya Talata, shugaban kasa ya baiwa ministan ilimi, Adamu Adamu umarnin ya warware takaddamar da ke tattare da yajin aikin ASUU cikin makwanni biyu.

Mun shirya kawo karshen yajin ASUU, inji gwamnatin Buhari

Sai dai, a wata sanarwa ta yau Laraba 20 ga watan Yuli da muka samu a shafin gwamnatin tarayya na Twitter, fadar shugaban kasar ta ce gwamnatin tarayya na fatan kawo karshen yajin aikin nan ba da dadewa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kuma yi karin haske kan matakin da aka dauka a taron na ranar Talata, inda ta kara da cewa ministan ne ya bukaci makwanni biyu zuwa uku don cimma yarjejeniya da kungiyar ASUU.

Hakazalika, sanarwar ta ce, gwamnatin tarayya a shirye take, kuma hannayenta a bude suke domin zaman sulhu da yanke shawari kan dawowar ASUU bakin aiki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

Sanarwar ta ce:

“A lokacin taro ko bayansa ba wani wa’adi da aka baiwa Ministan Ilimi.
“A yayin taron, Ministan Ilimi ya bukaci Ministan Kwadago ya mika masa tattaunawar don ba shi damar shugabanci tare da kammala abin da ya fara tun farko da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
"Kuma ya yi alkawarin cewa zai iya samar da yarjejeniya cikin kankanin lokaci mai yiwuwa makwanni biyu zuwa uku."
“A yayin aiwatar da wannan aiki, Ministan zai tafi tare da dukkan ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa tare da ayyuka na doka da ayyukan da suka shafi abubuwan da ke da alaka da yarjejeniyar.
“Fadar shugaban kasa na da kwarin gwiwar cewa za a iya cimma yarjejeniya cikin kankanin lokaci idan duk bangarorin masu ruwa da tsaki ba su kasance masu taurin kai ba. Muna kira ga bangarorin da su hada kai domin kawo karshen yajin aikin.
"A bangaren gwamnati, dukkan kofofi a bude suke domin tattaunawa da warware batutuwan."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya fusata, ya fadi ranar da yake so ASUU su janye yajin aiki

ASUU: Da 'ya'yan 'yan siyasa ne a jami'o'in gwamnati, da yajin mu ba zai kai kwana biyu ba

A wani labarin, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ce idan da ‘ya’yan ‘yan siyasa ne ke halartar jami’o’in gwamnatin Najeriya, yajin aikin kungiyar ba zai shafe kwanaki biyu ba.

Kamar yadda shafin jaridar The Cable ta ruwaito, kungiyar ta bayyana cewa wa'adin makwanni biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ministan ilimi Adamu Adamu ya yi yawa.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, yayin da yake hira da gidan talabijin na Channels.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.