'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a Abuja
- Yan bindiga sun kutsa kai har cikin gidan wani basarake a Abuja, sun yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da har yanzun ba'a gano ba
- Wani shugaban al'umma a yankin da abun ya faru ya ce maharan sun shafe kusan awa ɗaya amma babu wanda ya kawo ɗauki
- Kwamandan rundunar yan sanda na yankin Kubwa, ACP Muhammad Ndagi, ya ce sun fara bincike kan lamarin tun tuni
Abuja - Wasu miyagun 'yan bindiga da safiyar Lahadi, sun yi garkuwa da Dagacin Kuchibuyi, wani yanki mai nisa a ƙarƙashin Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Wani shugaba a yankin, wanda ya zanta da Daily Trust, ya ce an sace Malam Isiyaka Dauda a cikin gidansa, wanda ke nesa da fadarsa yayin harin yan bindiga.
Ya ce yan bindiga kusan su 10 sun buɗe wuta sau biyu suna dira gidan, hakan ya ankarar da Yan sa'kai, inda ya ƙara da cewa tilas yan Sa'kai suka takansu yayin da masu garkuwan suka nufe su.
A cewarsa maharan sun kutsa kai ta tsiya cikin wani ɗaki da ke cikin gidan, kafin daga bisani suka sake fasa wani ɗakin wanda suka samu Basaraken a ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sun yi awon gaba da shi ba tare da fuskantar wata tirjiya ba, kuma sun bi ta hanyar da zata kai mutum garin Bwari," a cewar mutumin.
Har zuwa jiya Litinin da yamma, babu wani rahoton da ke nuna cewa masu garkuwan sun tuntuɓi wani daga cikin iyalansa ko a yankin.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Kwamandan rundunar 'yan sanda na yankin Kubwa, mataimakin kwamishinan yan sanda ACP Muhammad Ndagi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yanzu haka jami'ai na kan bincike.
A wani labarin na daban kuma 'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar shugaban ƙasa ana ruwan sama, sun aikata ɓarna
Makonni kaɗan bayan kashe kwamandan yankin Dutsinma, yan bindiga sun yi garkuwa da mutum Tara a Shema Quaters.
Maharan sun yi awon gaba da matan aure hudu da kananan yara biyar a harin da suka kai cikin garin Dutsinma ana tsaka da ruwa.
Asali: Legit.ng