Dakarun sojoji sun dakile harin ta’addanci kan sansaninsu a jihar Neja

Dakarun sojoji sun dakile harin ta’addanci kan sansaninsu a jihar Neja

  • An gwabza tsakanin dakarun sojojin Najeriya da wasu yan ta'adda a garin Sarkin Pawa da ke karamar hukumar Munya ta jihar Neja
  • Yan ta'adda da ake zaton suna da alaka da Boko Haram sun yi yunkurin kai harin bazata kan sansanin soji da ke yankin amma sai suka tarar da dakarun sojin a shirye
  • Sojoji sun yi nasarar dakile harin bayan samun karin karfi daga Minna, babbar birnin jihar, lamarin da ya kai ga kashe mahara da dama

Niger - Dakarun sojoji sun dakile harin da wasu yan ta’adda da ake zaton suna da alaka da yan Boko Haram/ISWAP suka yi yunkurin kaiwa sansaninsu a Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Munya ta jihar Neja.

Yan ta’addan wadanda suka so kaiwa sojojin harin bazata sun isa yankin ne da sanyin safiyar Litinin, 18 ga watan Yuli, sai dai kuma jami’an tsaron sun zama cikin shiri inda suka nuna turjiya, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar shugaban ƙasa ana ruwan sama, sun aikata ɓarna

Yan bindiga
Dakarun sojoji sun dakile harin ta’addanci kan sansaninsu a jihar Neja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da harin a yau Litinin, kakakin gamayyar kungiyoyin Shiroro (COSA), Salis Sabo, ya bayyana cewa daruruwan ‘yan ta’addan sun zo yankin sannan suka yi kokarin tarwatsa sansanin sojojin.

Ya kuma bayyana cewa jami’an sojin sun yi musayar wuta da su a kimanin sa’o’i 2 har sai da aka samu karin karfi, lamarin da ya kaisu ga nasara har aka kashe yan bindiga da dama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake karin haske, Mista Sabo ya ce ya dauki karin sojojin kasa da sa’o’I 30 zuwa Sarkin Pawa daga Minna domin amsa kiran dakarunsu.

A cewarsa yadda jami’an tsaron suka fafata da maharan abu ne da ba’a taba ganin irinsa ba, inda ya kara da cewar hakan ya karfafa zukatan mutane da dama.

Sabo ya kuma ce rahoton da suka samu, ya nuna ba a rasa rai ba ta bangaren sojojin amma akwai alamu masu karfi cewa an kashe wasu yan ta’addan, koda dai ba a tabbatar da adadinsu ba.

Kara karanta wannan

Rundunar soji ta tsare jami’anta dake bakin aiki a lokacin harin gidan yarin Kuje

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, kakakin yan sandan jihar, DSP Abiodun Wasiu, yace ba shine ya kamata yayi magana kan lamarin ba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Wasiu ya tura wakilinsa zuwa ga kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, amma bai dauki wa yaba.

Mazauna garuruwan Plateau sun gudu daga gidajensu sakamakon wa’adin barin gari da yan bindiga suka basu

A wani labari na daban, al’ummar garuruwan da yan bindiga suka aikewa takarda a kwanan nan a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau sun tattara sun fice daga muhallinsu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jaridar Daily Post a ranar 29 ga watan Yuli ta rahoto yadda yan bindiga da yawansu suka ba mazauna kauyukan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwan Tsohon Soldier, Anguwan Yuhana da Anguwan Mangu a karamar hukumar wa’adin kwanaki biyar.

An bukaci mazauna yankunan da abun ya shafa da su bar garuruwan cikin kwanaki biyar ko kuma su fuskanci yaki.

Kara karanta wannan

Senata Ndume ya soki Buhari da hafsoshin tsaro akan harin gidan yarin Kuje

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel