Mazauna garuruwan Plateau sun gudu daga gidajensu sakamakon wa’adin barin gari da yan bindiga suka basu

Mazauna garuruwan Plateau sun gudu daga gidajensu sakamakon wa’adin barin gari da yan bindiga suka basu

  • Yan bindiga sun fitini al'ummar garuruwan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwan Tsohon Soldier, Anguwan Yuhana da Anguwan Mangu a karamar hukumar Wase
  • Jama'ar gari sun tattara yanasu-yanasu sun fice bayan an basu wa'adin mako guda ko a far masu da yaki
  • Rundunar yan sandan Plateau ta yi watsi da batun, ta ce jita-jita ne kawai kuma an tura jami'an tsaro zuwa yankin

Plateau - Al’ummar garuruwan da yan bindiga suka aikewa takarda a kwanan nan a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau sun tattara sun fice daga muhallinsu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jaridar Daily Post a ranar 29 ga watan Yuli ta rahoto yadda yan bindiga da yawansu suka ba mazauna kauyukan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwan Tsohon Soldier, Anguwan Yuhana da Anguwan Mangu a karamar hukumar wa’adin kwanaki biyar.

Kara karanta wannan

Yadda makiyaya suka tarwatsa kasuwar mako yayin da suke fada kan budurwa a wata jahar arewa

Jihar Plateau
Mazauna garuruwan Plateau sun gudu daga gidajensu sakamakon wa’adin barin gari da yan bindiga suka basu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An bukaci mazauna yankunan da abun ya shafa da su bar garuruwan cikin kwanaki biyar ko kuma su fuskanci yaki.

Wani mazaunin garin Pinau da ke da iyaka daya da garuruwan da abun ya shafa, Ubale Pinau, ya laburtawa ma jaridar Daily Trust cewa dukkanin kauyukan da yan bindigar suka lissafa sun zama kufai babu kowa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Babu ko mutum daya yanzu a garuruwan. Kowa ya tsere. Wasu mazauna garuruwan da abun yan shafa suna a Pinau yanzu haka yayin da wasu suka koma cikin garin Wase.
“Mutane na tsoron zama a garuruwan don gudun fushin yan bindiga. Koda dai akwai sojoji da aka zuba a Pinau, mazauna suna cike da tsoron abun da ka iya zuwa ya dawo.”

An tura sojoji da yan sanda yankin

Rundunar yan sandan jihar ta ce an tura jami’an sojoji da yan sanda zuwa garuruwa da ke yankin Wase.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar shugaban ƙasa ana ruwan sama, sun aikata ɓarna

Kakakin yan sandan jihar Plateau, Alfred Alabo, a ranar Litinin, ya karyata batun tura takardar barin garin da aka ce yan bindiga sun yi. Sai dai ya ce duk da haka an tura jami’an tsaro zuwa yankin.

A cewarsa, a lokacin da rundunar ta ji rade-radin aika takardar, sai aka tura sojoji da yan sanda zuwa wadannan garuruwa da kauyukan, Sahara Reporters ta rahoto.

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman Katolika 2 a Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da Limaman darikar Katolika guda biyu, Rev. Fr. John Mark Cheitnum da Rev. Fr. Donatus Cleopas, a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Chietnum ya kasance shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya a karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna, jaridar The Nation ta rahoto.

Da yake tabbatar da lamarin, Kansilan darikar Katolika a Kafancha, Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli, ya ce miyagun sun yi awon gaba da limaman ne a ranar Juma’a, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng