Kaduna: Gwamnatin El-Rufai ta sanar da ranar da za ta fara daukar malamai 10,000
- Yayin da aka kori wasu malamai da dama bisa zargin rashin cancanta, gwamnatin Kaduna za ta dauki sabbin malamai
- Bayanai sun bayyana yadda gwamnati ta tsara kafar yanar gizo domin fara daukar ma'aikata a ma'aikatar ilimi ta jihar
- A baya gwamna El-Rufai ya sanar da daura aniyar daukar malamai 10,000 domin kawo gyara a fannin ilimi na jiharsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da tsarin aiki na hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) na daukar malamai 10,000 ta kafar yanar gizo.
Wata sanarwa da Shugaban Hukumar KADSUBEB, Malam Tijjani Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa hukumar ta baiwa Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) aikin kirkira kafar daukar ma’aikata, wadda za ta fara aiki a ranar Alhamis, 21 ga Yuli, 2022.
Hakazalika, sanarwar ta ce masu bukatar cike fom din neman aikin dole ne su zama masu NCE da masu digiri na farko a fannin Ilimi (B.Ed, B.A EED, B.Sc, Bd, B.Tech daga jami'o'in da gwamnati ta amince dasu.
Yadda tsarin zai kasance
Hakazalika, rahoton ya ce, za a bude kafar na tsawon makonni biyu daga ranar ranar 21 ga Yuli, 2022, zuwa 5 ga Agusta, 2022.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A bangare guda, bayan kammala cike fom din, sanarwar ta ce za a gudanar da kwarya-kwaryar jarrabawar tantancewa ta yanar gizo a garuruwa uku na jihar da suka hada da Kaduna, Zaria da Kafanchan.
Da yake magana kan yadda za a bi wajen tantance nasarar wadanda suke neman aikin, ya ce:
“Wadanda suka samu 75% a jarrabawar, wanda shi ne ma’aunin da gwamnatin jihar Kaduna ta tsara, za a gayyace su ne domin tattaunawar baki da baki.”
Malam Tijjani ya kuma ce ana sa ran wadanda suka yi nasara za su zo da asali da kwafin takardunsu a wurin tattaunawar. Za a duba ainihin takardun yayin da za a ba da kwafinsu ga kwamitin tantancewa.
Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa hukumar ta KADSUBEB za ta aike da dukkan kwafin takardun nan take zuwa makarantu daban-daban domin tantancewa.
A cewarsa, wadanda suka yi nasara za a dauka aiki sannan kuma KADSUBEB za ta buga sunaye da bayanan wadanda aka dauka aiki.
Hakazalika, hukumar ta ce za ta tabbatar da tura malaman bangarori daban-daban na jihar, ciki har da kauyuka da karkara.
El-Rufai zai dauki malamai 10,000 aiki bayan ya kori sama da 2,000
A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kammala shirin daukar malaman firamare 10,000 domin maye gurbin wadanda aka kora domin inganta alakar malamai da dalibai, Daily Trust ta ruwaito.
Mataimakiyar gwamnan, Dakta Hadiza Balarabe ce ta bayyana haka a Kaduna, a jiya, a wajen kaddamar da rabon kayayyakin koyo ga dalibai a makarantun firamare na gwamnati 4,260 da kuma cibiyoyin koyo 838.
A ranar 19 ga watan Yuni ne gwamnatin jihar ta sanar da korar malaman makarantun firamare 2,357 saboda rashin cin jarabawar cancanta da gwamnati ta yi musu, lamarin da ya jawi cece-kuce daga kungiyar malamai, inji Vanguard.
Asali: Legit.ng