Likitoci sun yi maganar halin da Osinbajo yake ciki bayan an yi masa aiki a kafa
- Likitoci sun tabbatar da cewa an yi wa Farfesa Yemi Osinbajo aiki lafiya kalau a kafafun da ke damunsa
- An yi wa Mataimakin shugaban kasar Najeriyan aiki ne a asibitin Duchess International a Legas
- Shugaban asibitin, Dr. Adedoyin Dosunmu-Ogunbi ya ce nan da ‘yan kwanaki ne za su sallami Osinbajo
Lagos - Likitocin da suka duba Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo saboda matsalar kafafu, sun tabbatar da cewa sun yi masa aiki cikin nasara.
A jiya ne Mai magana da yawun Mataimakin shugaban Najeriyar, Laolu Akande ya shaidawa The Guardian cewa Farfesa Yemi Osinbajo yana nan garau.
Shugaban asibitin na Duchess International da ke garin Ikeja, a jihar Legas, Dr. Adedoyin Dosunmu-Ogunbi, ya fitar da jawabi na musamman da ya yi wa take da “An yi nasara yiwa Mataimakin shugaban kasa aikin tiyata”.
Dr. Adedoyin ya tabbatar da cewa an yi dace wajen aikin na su.
Legit.ng Hausa fa fahimci Dr. Adedoyin Dosunmu-Ogunbi ya fitar da jawabin a shafin Twitter.
An yi aiki lafiya - Dr. Dosunmu-Ogunbi
“An kwantar da Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Professor Yemi Osinbajo, SAN, GCON a asibitin Duchess International Hospital GRA, Ikeja, Legas a yau a dalilin gurdewa da ya samu a kashin cinya da ke alaka da yawan tsayuwa wajen buga wasan Squash.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Likitocin da suka yi aikin
An yi masa aiki a karkashin jagorancin kwararrun likitoci da suka hada da Dr. Wallace Ogufere (Kwararren Likitan kashi); Dr. Om Lahoti (Kwararren Likitan kashi); Dr. Babajide Lawson (Kwararren Likitan kashi); da Dr. Ken Adegoke (Kwararren Likitan fida); Dr. Oladimeji Agbabiaka (Kwararren Likitan fida); and Dr Adedoyin Dosunmu-Ogunbi (Kwararren Likita kuma shugaban asibiti)
An yi aiki, an kammala lafiya kalau, ana sa ran za a sallame shi nan da ‘yan kwanaki kadan."
A rahoton da ya fito daga Punch, wata majiya ta bayyana cewa an ji cewa Farfesa Osinbajo ya zabi wannan asibiti ne domin ya yarda da Likitocin Najeriya.
Majiyar ta ke cewa an ba mataimakin shugaban kasan shawara ya bar Najeriya, amma ya hakikance a kan cewa kwararrun Najeriya ne za su duba kafafun.
Sanarwar kwantar da Osinbajo
A baya mun kawo rahoto Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yana kwance a asibiti, ana sa ran cewa za ayi masa aiki a kafafu.
Tun 2015, ba kasafai aka saba jin Osinbajo mai shekara 65 da haihuwa bai da lafiya ba.
Asali: Legit.ng