Matashi ya aika wa matar aure sakon soyayya, mijinta ya yi masa mugun duka, 'yan sanda sun yi martani

Matashi ya aika wa matar aure sakon soyayya, mijinta ya yi masa mugun duka, 'yan sanda sun yi martani

  • Wani matashi ya yi wa 'yan sanda magana a Twitter kan yadda ya turawa matar aure sakon yana son ta amma mijinta ya je ya lakada masa duka
  • Sai dai martanin da 'yan sandan suka bada ya birge jama'a inda suka ce yayi laifi, sai dai dama mijin matar ya mika musu matashin, sai su yi masa abinda doka ta tanada
  • Har ila yau, 'yan sandan sun bukaci matashin da ya kai kansa ofishin 'yan sanda mafi kusa, wanda hakan yasa yayi saurin goge wallafar da yayi a Twitter

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, ya bukaci taimakon 'yan sanda bayan wasu sun yi masa mugun duka don ya tura wa matar aure cewa yana son ta.

A wallafarsa ta Twitter wacce yanzu aka goge, mutumin mai suna Sushant Dutt yayi ikirarin cewa wani mutum ya lakada masa bakin duka bayan yace yana son matarsa.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta

'Yan sandan Punjab
Matashi ya aika wa matar aure sakon soyayya, mijinta ya y masa mugun duka, 'yan sanda sun y martani. Hoto daga indiatoday.in
Asali: UGC

Sushant ya kara da bayyana cewa, bayan lamarin ya faru, sai ya fara tsoron halin da zai iya shiga a gaba kuma hakan yasa ya roki 'yan sandan Punjab da su ceci rayuwarsa.

"Ranka shi dade, na tura wa wata cewa ina son ta amma mijinta ya iske ni kuma ya lakada min duka a daren jiya, ina ta bada hakuri. Amma yanzu ina tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. Ku taimake ni, ku ceci rayuwata, ta yuwu yau ma su sake kawo min farmakin," ya rubuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda Punjab sun ga rokon inda suka yi masa martani da wuri.

"Bamu san me kake tsammani ba da ka yi wa matar haramtaccen sakon, amma bai dace su dake ka ba," 'yan sandan suka ce.
"Da sun kawo mana rahoto kuma mu yi maka abinda ya dace a karkashin tanadin doka. Dukkan laifukan nan zamu magancesu kamar yadda doka ta tanada," suka cigaba da cewa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda na asirce mijina, babu wacce ta isa ta kwace min shi, Matar aure ta sanarwa duniya

A wata wallafar da 'yan sandan Punjab din suka yi, sun bukaci Sushant da ya kai kansa ofishin 'yan sanda mafi kusa kuma ya mika korafinsa.

Tuni dai wallafar ta janyo jinjina da tsokaci masu yawa daga jama'a wadanda suka garzaya sashin tsokaci domin fadin ra'ayinsu, India Today ta ruwaito.

Wasu sun jinjinawa 'yan sandan kan martaninsu yayin da wasu suka yabawa mijin matar wanda suka ce yayi daidai a hukuncin da ya dauka.

'Dan majalisa na zargin mai magana da yawun majalisar wakilai da neman matarsa

A wani labari na daban, Robinson Uwak, tsohon 'dan majalisar wakilai ya jaddada cewa mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu, yana da wata alakar cin aman da matarsa mai suna Keiza Uwak.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Uwak yayin martani ga wasika mai kwanan wata 17 ga Yulin 2022, ta hannun lauyansa, inda Kalu ya bukaci ya janye wannan mummunan zargin tare da bashi hakuri.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng