Bidiyo: Yadda na asirce mijina, babu wacce ta isa ta kwace min shi, Matar aure ta sanarwa duniya

Bidiyo: Yadda na asirce mijina, babu wacce ta isa ta kwace min shi, Matar aure ta sanarwa duniya

  • Wata matar aure ta janyo cece-kuce bayan ta fitar da bidiyonta tare da mijinta wanda tace ta asirce kacokan har abada
  • Matar auren wacce tace mijinta 'dan kasar Kamaru ne, tace a kwalbar tsafi ta saka shi shiyasa bai isa ya ci amanarta ba
  • Ta kara da cewa, babu macen da ta isa ta kwace shi saboda biyayya yake mata, amma ita a gabanshi take cin amanar shi kuma baya iya tankawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matar aure ta janyo maganganu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan ta fallasa boyayyen sirin dake tattare da ita.

Tace ta kulle mijinta 'dan kasar Kamaru a kwalbar tsafi, wanda hakan yasa yake mata biyayya kuma ba zai taba iya kula wata mace ba a rayuwarsa.

Matar aure
Bidiyo: Na asirce mijina, babu wacce ta isa ta kwace min shi, Matar ta sanarwa duniya. Hoto daga @onejoblessboy
Asali: Twitter

Matar auren bata tsaya nan ba, ta wallafa bidiyonta da mijinta mai suna Michael kuma tace saboda kwalbar tsafin da ta rufe shi a ciki ne yasa baya iya cin amanarta yayin da ita kuwa take cin tashi amanar.

Kara karanta wannan

'Dan uwan ango ya bindige amarya ana tsaka da shagalin biki, ta sheka lahira

A bidiyon da @OneJoblessBoy ya wallafa a Twitter, ta kara da bayyana irin karfin da tsafin yake da shi wanda tayi amfani da shi kan mijin wanda tace ko kusa da kwace shi wata ba za ta iya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama'a sun yi martani

@PedroAisosa yace: "Kai, wannan dai talla ne kawai."
@riki yace: "Yesu, na taba ganin irin wannan mafarkin lokacin ina yaro. Babu wani makamai da zai iya tasiri a kaina."
@Izzulabell: "A nema wa Michael 'yancinsa, dole mu ceto wannan 'dan uwan."

Wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa da ta kai kwarto daki, tana kokarin fitar dashi

A wani labari na daban, wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa yayin da ta gama shagalinta da kwartonta kuma tana son fitar da shi daga gidan.

Makwabcin wanda ya ga abinda ya faru kuma ya yanke hukuncin nadar lamarin a wayarsa daga dakinsa, ya bayyana irin cin amanar da matar tayi wa mijin ta.

Kara karanta wannan

Kin fi karfi na: Miji ya fece ya bar matarsa saboda ta haifa masa tagwaye sau biyar

Ma'auratan suna zama ne a rukunin gidaje wanda ke dauke da dakunan mutane da yawa, hakan ne yasa fitar kwarton matar ya nemi ya basu wuya.

Idan yace zai diro shine kawai hanyar da zai fita cikin sauki, amma kuma kwarton ya bayyana a rude kuma tsoro ya bayyana a fuskarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel