Wata sabuwa: Babu wata yarjejeniya tsakanimu da ASUU, inji gwamnatin Buhari
- Gwanbatin Najeriya ta magantu kan tushen yarjejeniyar ta kungiyar malaman jama'o'i ta Najeriya wato ASUU
- Gwamnati ta ce, sam bata san da wata yarjejeniya tsakaninta da ASUU ba, don haka a sake duba batutuwan
- A bangare guda, ASUU a baya ta yi ikrarin zama da jami'an gwamnati, kana ta nemi shugaban kasa ya kawo mafita ta hanyar sanya hannu a yarjejeniya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce babu wata yarjejeniya ta hadin gwiwa (CBA) tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’i wao ASUU da ke jiran sa hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Olajide Oshundun, ya fitar ranar Laraba, inji Daily Trust.
A cewar wani yanki na sanarwar da ke rusa bayanin yarjejejiyar hadin gwiwar maslaha tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU, ma'aikatar kwadagon ta ce:
“Abin da ke kasa shine shiri. Ko a lokacin da aka yi irin wannan CBA, ba shugaban kasa ne ya sanya hannu ba. Daga bayanan da ake da su, babu wani shugaban Najeriya ko wani mai mulki da ya yi hakan.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ministan ya zargi ASUU da kayyade albashi da alawus-alawus din ta wani kwamitinta ba tare da tsoma ma’aikatu da hukumomin gwamnati da kuma ofishin shugaban ma’aikata da ke da alhakin tabbatar da irin wannan shawara ba.
Ya bayyana cewa, shawarar kwamitin Farfesa Nimi Briggs na karin 109% -185% na tsarin albashin jami’o’in zai karawa gwamnatin tarayya nauyin N560bn a matsayin albashi kadai baya ga N412bn da take kasuwa kan malaman a yanzu, rahoton Vanguard.
Ya kara da cewa za a bukaci N1.12tn domin biyan albashi da alawus-alawus na malaman jami’o’i da sauran ma’aikata a jami’a.
Ngige ya ce wannan bayanin ya zama wajibi ganin yadda shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke da shugabannin reshe ke yaudarar ‘yan Najeriya da gangan.
Hakazalika, ya zargi shugabannin na ASUU da matsawa shugaban kasa da ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da suka ce sun cimma da gwamnatin tarayya.
Tsagin ASUU ya magantu kan martanin Buhari
Shugaban ASUU a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Talata a Abuja ya ce:
“Ban fahimci dalilin da ya sa shugaban kasa ya ce ‘ya isa haka ba’ alhali ba mu ne ke jinkirta zaman dalibai a gida ba.
“Gwamnatin tarayya ta aiko da tawagarta domin tattaunawa da mu kuma mun gama. Maimakon su dawo wurinmu su gaya mana sakamakon zaman, sai kuma muka ji haka.
“Idan kun kafa kwamiti don tattaunawa a madadinku, to kwamitin ya gama kuma sun kawo muku bayanan ku sanya hannu, sannan kuka ce ya isa, me wannan ke nufi.”
Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su sake duba matsayar su kan yajin aikin da suka dade suna ciki.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ‘yan majalisa da shugabannin siyasa a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ta fahimci matsayarsu, kuma za ta ci gaba da tattaunawa dasu, amma dai dalibai su koma makaranta, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng