‘Yan ta’adda sun fito fili su na yi wa mutane wa’azin yaki da Gwamnati a Birnin Gwari
- Kungiyar Jamā’atu An’āril Muslimīna fī Bilādis Sūdān sun bi kauyuka su na yin wa’azi a Kaduna
- Kiran da ‘Yan kungiyar ta Ansaru suke yi shi ne mutane su gujewa mulkin farar hula da ilmin boko
- ‘Yan ta’addan sun yi kira ga mazauna kauyukan Birnin Gwari da su tanadi makaman yaki
Kaduna - Wasu daga cikin ‘yan kungiyar ta’addan nan na Ansaru, sun fito bainar jama’a, su na yin wa’azi a wasu kauyukan da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Wani rahoto mai ban tsoro da ya fito daga Daily Trust ya bayyana cewa’yan ta’addan sun yi amfani da lokacin bikin babbar sallah, wajen karkatar da Bayin Allah.
Wani mazaunin Birnin Gwari ya fadawa ‘yan jaridar cewa ‘Yan kungiyar Ansaru su na kokarin fadakar da mutane ne domin su bi irin salon addinin da suke yi.
‘Yan ta’addan su na yin wa’azi ne a kan sharrin tsarin damukaradiyya da ilmin boko, tare da yin kira ga al’umma da su yi tawaye da duka hukumomin gwamnati.
Baya ga haka, ‘yan kungiyar Ansaru sun yi alkawarin kare mutanen yankin daga ta’adin ‘yan bindiga.
Wata majiya ta ce tun a ranar da aka yi sallar idi (Asabar), wadannan mutane suke yin wa’azi a kauyuka domin bijirewa gwamnati da tsarin mulkin farar hula.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ansaru sun shiga Kauyuka
‘Yan kungiyar sun ziyarci kauyukan da ke karkashin karamar hukumar Birnin Gwari irinsu Damari, Unguwar Gajere, Kakini, Kuyello da kuma Kwasa Kwasa.
Kamar yadda rahoton da aka fitar ranar Laraba ya nuna, haka wadannan ‘yan ta’adda suka fito bainar jama’a su na yin kira, ba tare da an taka masu burki ba.
Jawabin wani Mazaunin yankin
“’Yan ta’addan wadanda mafi yawansu matasa ne, su na yawon wa’azi ne a tulin babura dauke da tutoci da aka yi rubutu da harshen larabci.”
“Sun caccaki hukumomin gwamnatin tarayya, na jihohi da kananan hukumomi, su na cewa damukaradiyya ya sabawa koyarwar addini.”
“Sun kuma soki Malaman Musulunci da ke umarnin ayi wa shugabannin farar hula addu’o’i.”
Majiyar ta ce abin da ya fi hadari shi ne kiran da ‘yan ta’addan suke yi wa jama’a na tanadar makamai domin su yaki gwamnati ta hanyar murda hujjojin Islama.
Fasinjojin AK29
Ku na da labari Daloli da makudan miliyoyi suka yi aiki kafin a saki mutum 7 cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja da miyagun ‘yan ta’adda suka dauke a watan Maris.
An fahimci cewa ‘yanuwan wadanda aka dauke sun biya N600m, shi kuma wani ‘Dan kasar waje da ya shiga hannunsu, sai da ya bada N200m kafin ya iya fitowa.
Asali: Legit.ng