Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU
- An baiwa shugabannin kungiyar malaman jami’o’i umarnin kawo karshen yajin aikin da suke yi a halin yanzu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya mika wa kungiyar wannan umarni a wata ganawa da wasu manyan 'yan APC
- A cewar shugaban, ya kamata ASUU ta tausayawa dalibai, iyaye da ‘yan Najeriya baki daya su koma kbakin aikinsu
Daura, jihar Katsina - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su sake duba matsayar su kan yajin aikin da suka dade suna ciki.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ‘yan majalisa da shugabannin siyasa a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ta fahimci matsayarsu, kuma za ta ci gaba da tattaunawa dasu, amma dai dalibai su koma makaranta, rahoton Vanguard.
Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya nuna damuwarsa kan cewa yajin ke haifar da illa ga iyalai da tsarin ilimi da kuma ci gaban kasar a nan gaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban ya ce tuni yajin aikin ya yi illa ga tarbiyyar da iyaye ke ba dalibai da sauran masu ruwa da tsaki, lamarin da ya jefa al’amuran da’a cikin wani yanayi.
Buhari ya ce makomar kasar ta dogara ne kan ingancin cibiyoyin ilimi da karantarwa.
A cewar Buhari:
“Muna fatan ASUU za ta tausayawa jama’ar game da yajin aikin nan maii tsawo. Hakika, ya isa ci gabada ajiye dalibai a gida, kada ku cutar da 'yan baya don Allah.
“Ta hanyar fasaha, muna da dama sosai. Ya kamata mu kwadaitar da yaranmu su samu ilimi, ba wai kawai neman aikin gwamnati ba."
Saura kiris yajin aikin ASUU ya zo karshe, FG ta bayar da tabbaci
A wani labarin, karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin kawo karshen yajin aikin malaman jami’a (ASUU) nan bada jimawa ba.
Ministan ya bayar da tabbacin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a karshen mako yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wani liyafa da abokansa suka shirya masa.
Ya ce: “Zan iya tabbatar maku cewa gwamnati ta damu sosai game da lamarin. Har yanzu da nake magana da ku tunane-tunane da dama, tattaunawa da dama da taruka na gudana da nufin magance lamarin cikin gaggawa."
Asali: Legit.ng