Da Dumi-Dumi: Akwai matuƙar wahala, na ƙosa na kammala wa'adina, Buhari ya koka

Da Dumi-Dumi: Akwai matuƙar wahala, na ƙosa na kammala wa'adina, Buhari ya koka

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ba ƙaramar wahala ya ke sha ba domin ya kosa wa'adin mulkinsa ya ƙare ya koma Daura
  • Da yake jawabi ga gwamnonin APC da wasu shugabannin siyasa, Buhari ya ce ya gode Allah mutane sun yaba da ƙoƙarinsa
  • Game da rashin tsaro, shugaban ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori a wasu sassan Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Daura, jihar Katsina - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ya ƙosa ya miƙa wa magajinsa mulkin Najeriya saboda, "ya sha matukar wuya." kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƙasan ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi baƙuncin gwamnonin jam'iyyar APC, yan majalisu da jagororin siyasa a gidansa da ke garin Daura, jihar Katsina, ranar Litinin.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Da Dumi-Dumi: Akwai matuƙar wahala, na ƙosa na kammala wa'adina, Buhari ya koka Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Buhari ya bar fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja zuwa mahaifarsa wato Daura a ranar Jumu'a domin gudanar da shagulgulan babbar Sallah (Eid-el-Kabir) a gida.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU

Shugaban ƙasan ya gargaɗi baƙinsa cewa su yi takatsantsan wajen taimaka wa mafi yawan 'yan Najeriya da ke neman samun wasu damarmaki don su dama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa, Buhari ya ce:

"A irin wannan lokacin na shekara mai zuwa na cimma ƙarshen zangon mulki na guda biyu kuma sauran 'yan watannin da suka rage, zan yi iya kacin bakin kokari na."

Buhari ya shaida wa gwamnoni da kuma jagororin siyasa cewa rabonsa na zuwa gidansa na Daura kusan shekara ɗaya kenan kuma ba don komai ba sai don aikin Ofis.

Ya ƙara da cewa da zaran ya gama wa'adin mulkinsa zai koma gidansa na Daura da zama ba wai Kaduna ba inda ya ke da babban gida.

"Ina wa duk mutumin da zai karɓi Najeriya bayan na gama fatan nagari," inji shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 22 zasu tabbatar jam'iyyar APC ta lashe zaɓen 2023 a jihohin su, Gwamna ya faɗe su

Ina aka kwana game da matsalar tsaro a Najeriya?

Game da matsalolin tsaro, Shugaban ƙasa ya ce arewa maso yamma ne ke fama da kalubalen rashin tsaro, amma gwamnatinsa ta samu nasara sosai a sauran sassan ƙasar nan kamar arewa maso gabas da kudu maso kudanci.

"Na ƙagara na tafi, zan iya faɗa muku cewa na sha wahala. Ina gode wa Allah saboda mutane suna yaba wa da sadaukarwar da muke yi."

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 9 a Daura

Gwamnonin cigaba na jam'iyyar APC guda Tara sun kai ziyarar barka da Sallah ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.

Bayan ganawar sirri da Buhari, gwamnonin sun bayyana cewa Tinubu da Shettima za su kara haskaka cigaban APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262