Yadda ‘Yanuwa suka biya N800m kafin su ceto Fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
- Ba a banza ‘Yan ta’adda suka fito da wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ba
- Tun a watan Maris ‘Yan ta’adda suke tare jirgin, suka yi awon-gaba da wasu daga cikin matafiya
- A makon da ya wuce aka saki mutane bakwai, an fahimci sai da ‘yanuwansu suka biya N800m
Kaduna - Naira miliyan 800 aka biya kafin ‘yan ta’addan da ke tsare da fasinjojin AK29 su saki wasu karin mutane bakwai da ke hannunsu a ranar Asabar.
Daily Trust ta fitar da wani rahoto da ya bayyana cewa ‘yanuwa da makusantan wadannan mutane da suka kubuta, sun biya kudin fansa na Naira miliyan 800.
Har yanzu babu kungiyar da ta dauki nauyin yin garkuwa da fasinjojin. Masana sun ce ‘Yan Boko Haram ne ko ISWAP, wasu kuma na zargin ‘yan bindiga ne.
Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa sai da aka biya Naira miliyan 100 a kan kowane mutum.
'Dan kasar waje ya biya N200m
Shi kuma Muhammad Abuzar wanda mutumin kasar Fakistan ne, ya kubuta ne bayan an biya Naira miliyan 200 a kan sa, kudin fansarsa ya fi na kowa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta ce ‘yan ta’addan sun karbi Nairori da kuma Dalar Amurka. N200m kadai aka karba a kudin Naira, an biya sauran N600m ne cikin Dalar Amurka.
Dole 'Yanuwa su ka nemi kudi
‘Yanuwam wadannan mutane sun zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da halin da masoyansu suke ciki, don haka suka saida kadarorinsu domin su tara kudi.
Shi ma wani wanda abin ya shafi danuwansa, ya ce gwamnati ba za ta damu idan an kashe mutanen da aka dauke ba, hakan ta sa dole suka nemi kudin fansarsu.
Wasu na tsare har gobe
Legit.ng Hausa ta samu labari daga wata majiyar cewa sai da iyalai da ‘yanuwan wadannan Bayin Allah suka bada Naira miliyan 100 kafin a iya ceto su.
Irinsu Farfesa Abdulaziz Attah wanda mahaifiyarsa da yayarsa su na cikin wadanda aka tare a jirgin kasan, har yanzu bai yi ido hudu da su ba, su na tsare.
Mahaifiyar wannan malamin makaranta ta manyanta, ta haura shekara 80 a Duniya amma hakan bai sa ‘yan ta’addan sun ji tausayin irin halin da take ciki ba.
Tukur Mamu ya taka rawar gani
A baya kun samu rahoton cewa bayan an dade ana tattaunawa, an yi nasarar ceto wasu daga cikin fasinjojin da aka dauke a jirgin Abuja zuwa Kaduna.
Hadimin Dr. Ahmad Gumi watau Malam Tukur Mamu (Dan-Iyan Fika) shi ne ya taka rawar gani wajen ganin ‘yan ta’adda sun fito da wadannan mutane.
Asali: Legit.ng