Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

  • Kwararren a bangaren halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Dutse, Dakta Sadiq Amali ya ce ya gargadi ministan harkokin cikin gida game da yiwuwar hari
  • Dakta Amali ya ce ya janyo hankalin Rauf Aregbesola a lokacin da gwamnati ke sakin fursunoni da nufin rage cinkoso yayin annobar korona
  • A cewar Amali, za a cigaba da samun hare-hare a gidajen gyaran halin muddin gwamnati ba ta dauki matakan inganta tsaro da tattara bayanan sirri ba

Dakta Sadiq Amali na sashin nazarin halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Jigawa ya bayyana cewa ya yi hasashen za a kai hari gidan yarin Kuje a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Yayin da ya ke magana kan harin a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Dakta Amali ya ce ya rubuta wasika ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbsola, game da yiwuwar kai harin.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Harin Kuje
Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dr Sadiq. Hoto: Fadar Shugaban Najeriya.
Asali: Twitter

Yan bindiga da ake kyautata zaton yan ta'adda ne, daruruwansu sun kai hari gidan yarin a ranar Talata da dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jimillar fursunoni 879 ne suka tsere yayin harin kuma kimanin 70 cikinsu wadanda ake zargin yan Boko Haram ne.

Kwararre a bangaren tsaron ya ce idan hukumomi ba su dauki mataki ba, hare-haren za su cigaba da faruwa.

"Na tuntubi minista (harkokin cikin gida) da kwantrola janar na gidajen gyaran hali kan yawaitan hare-haren gidan yari a kasar.
"A lokacin da suke rage cinkoso a yayin annobar korona, na yi magana a hukumance da ministan kuma na bashi shawara kan hatsarin rage cinkoson gidajen yarin.
"Idan ka saki (fursunoni) suka koma cikin mutane za su hada baki da wasu bata gari kuma su yi kokarin fito da takwarorinsu da ke tsare.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Tsohon Firaministan Japan da aka harba a ranar Alhamis ya rasu a Asibiti

"Na san hakan za ta faru, ministan ya amsa shawarwarin da na bada watakila matakan da aka dauka ba su isa bane, ko kuma akwai wani nau'in sakaci a bangaren ma'aikatan gidan yarin."

Yayin da ya ke bayyana harin a matsayin abin kunya ga kasa, kwararren a bangaren gyaran tarbiyan masu laifi ya dora laifi kan hukumomin tattara bayanan sirri a Najeriya.

Ya kuma ce akwai koma baya a bangaren tsaro a gidajen gyaran hali a kasar, yana mai kira ga gwamnati ta dauki matakan gyara don rufe gibin da ke akwai.

Harin Kuje: Kun Bani Kunya, Buhari Ya Fada Wa Hukumomin Tattara Bayanan Sirri

A wani rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadinsa da hukumomin tattara bayanan sirri, bayan harin da yan ta'adda suka kai gidan yarin Kuje, Daily Trust ta rahoto.

Bayan zagawa ya duba wurin da aka kai harin a ranar Laraba, "hukumomin tattara bayanan sirri sun bani kunya. Ta yaya yan ta'adda za su shirya, su taho da makamai, su kai hari wurin da jami'an tsaro suke kuma su tsere?

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164