Yanzu-Yanzu: Gwamnatin jiha ta rushe cocin wani fitaccen faston da ake kai ruwa rana dashi
- Fitaccen fasto a jihar Anambra ya rasa ginin cocinsa yayin da aikin gyaran birni ya biyo ta kan cocin
- Gwamnatin jihar Anambra karkashin Charles Soludu ta fara aiwatar ayyukan tsara birnin Onittsha tun bayan hawansa
- An ga bidiyon da ke nuna lokacin da faston ke kokarin hana ma'aikatan rushe cocin, amma lamarin ya ci tura
Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta rusa cocin Mountain of Holy Ghost Intervention and Deliverance da ke hannun fasto Chukwuemeka Ohanaemere da aka fi sani da ‘Odumeje’ a birnin kasuwanci na Onitsha.
Hakan ya yi daidai ne da shirin sabunta birnin Onitsha wanda Gwamna Charles Soludo ya fara a kwanan nan, Leadership ta ruwaito.
An ce an gina ginin tare da rafin Nwagene kuma dole ne a cire shi don aiwatar da shirin sabunta biranen na Onitsha.
Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da jami'an gwamnati suka kama faston yayin da yake yunkurin dakatar da aikin rushewar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tribune Online ta tattaro cewa cocin Odumeje a watan Maris din wannan shekarar ne gwamnatin jihar Anambra ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin gine-ginen da ke zaune kan magudanan ruwa, kuma aka sanya masa alamar rugujewa.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya ziyarci garin Okpoko da ke Onitsha kwana guda bayan rantsar da shi, ya kuma yi alkawarin tsaftace yankin ta hanyar tabbatar da samar da isassun magudanan ruwa.
Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama
A wani labarin, majiyoyin tsaro, a ranar Laraba, sun bayyana cewa sojojin da aka tura yankin Kuje da kewayen magarkama, wadanda suka yiwa yankin farin sani, an sauya musu mazauni sa’o’i 24 kafin ‘yan ta’adda su kai hari gidan yarin Kuje.
Majiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa aka kwashe su jami'an da suka san yankin sa'o'i 24 kafin harin, kuma har yanzu ba a samun wasu da suka maye gurbinsu ba har 'yan ta'addar suka far wa yankin, inji Vanguard.
Sai dai kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wa'adin da ya kamata sojojin su zauna a wannan yankin ya wuce kuma dama ya kamata a sauya su.
Asali: Legit.ng