Zargin safarar sassan Jiki : Ike Ekweremadu Ya Koma Kotu

Zargin safarar sassan Jiki : Ike Ekweremadu Ya Koma Kotu

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya koma Kotun a kasar Burtaniya domin cigaba da shariar sa
  • Hukumomin yansanda kasar Burtaniya suna zargin Ekwerenmadu da matar sa da laifin safarar mutane da kuma girbin sassan jikinsu
  • Senata Ekwerenmadu yana da yarinayar da take fama da ciwon koda kuma tana bukatar a yi mata dashe

Burtaniya - Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya koma Kotun Majistare na kasar Burtaniya domin ci gaba da shari’ar sa. Rahoton Channels Tv

Rundunar ‘yan sandan Birtaniya ta kama Ekweremadu da matarsa, Beatrice a ranar 23 ga watan Yuni bisa zargin safarar mutane da kuma girbin sassan jikinsu da suka saba wa dokar bautar zamani ta kasar.

Hukumomin ‘yan sandan dai sun zargi dan majalisar da hada baki wajen kawo wani yaro dan Najeriya mai shekaru 15 zuwa kasar Birtaniya domin girbin gabobin sa, .

Kara karanta wannan

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

ike ekwe
Zargin safarar sassan Jiki : Ike Ekweremadu Ya Koma Kotu : FOTO Legit.Ng
Asali: UGC

Da take bayar da karin haske daga harabar kotun a ranar Alhamis, wakiliyar Channels Television, Juliana Olayinka, ta ce akwai nuna goyon baya daga offishin jakadancin Najeriya a Burtaniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce dan majalisar na iya zuwa Najeriya don kare kansa a kotu ko kuma a ci gaba da tsare shi a hannun 'yan sandan Birtaniya.

Ta bayyana cewa dan majalisar da ke wakiltar mazabar Enugu ta Yamma yana da diya mara lafiya da take fama da ciwon koda kuma tana bukatar a yi mata dashe.

“Abin da muka sani game da al’amarin shine wasu sun dauko wani matashi mai shekaru 15 daga kan titin Legas da nufin girbar gabobin jikin sa,” in ji ta.

A jiya ne dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar NIMC da ta mika Certified True Copy (CTC) na bayanan yaron da aka kai burtaniya da mika shi zuwa kasar Burtaniya don taimaka wa Ekweremadu. kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Kara karanta wannan

An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi murabus daga shugabancin jam’iyyar sa

Ingila - A Yau Alhamis ne Firaministan Birtaniya Mista, Boris Johnson zai sauka daga mukamin shugabancin jam’iyyar ta Conservatives. Rahoton BBC HAUSA

Mista Johnson zai cigaba da zama firaministan kasar har zuwa watan Oktoba.Yanzu za a nada sabon shuagaban jam’iyyar Conservative da zai maye gurbin sa, sannan a zabi sabon Firaminista a watan Oktoba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa