Yanzu-Yanzu: 'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje
- A daren ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa magarkamar Kuje ta Abuja hari da bama-bamai, kamar yadda hukumar NCoS ta tabbatar da harin a ranar Laraba
- A yammacin ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci wurin da lamarin ya faru inda ya bayyana fusatarsa da lamarin
- A wani sabon al'amari, kungiyar ISWAP a martaninta, ta dauki alhakin kai harin, har ma ta fitar da wani faifan bidiyo don tabbatar da ikirarinta
Kungiyar ‘yan ta’addan SWAP ta dauki alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja, rahoton Daily Trust.
Rahotanni a baya sun bayyana yadda ‘yan ta’adda suka kutsa cikin gidan yarin, a daren ranar Talata, inda suka saki fursunoni sama da 800, ciki har da manyan mutane da ke tsare a ciki.
A wani faifan bidiyo da aka gani a daren Laraba, kungiyar ta'addancin ta nuna wasu daga cikin mutanenta suna harbi kan hanyarsu ta shiga cikin ginin magarkamar.
An gomman mayaka suna tafiya cikin dandazo yayin da motoci da gine-gine ke ci da wuta a cikin bidiyon da bai wuce dakika 38 ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, an ga wani dattijo da ke sanye da kayan gargajiya shi ma ya bi sahun samarin da ke ta ihu a cikin tsagerun.
Kafar labarai ta A’maq Agency ce ta fitar da bidiyon tare da rubutu ta harshen larabci cewa:
"A jiya ne mayakan kungiyar IS suka kai hari gidan yarin Kuje dake Abuja inda suka yi nasarar kubutar da fursunoni da dama."
Tun da farko, da ya ziyarci gidan yarin a safiyar Laraba, Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce maharan kai tsaye suka nufi hanyar da ake ajiye wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne.
Magashi ya ce bayan harin ba a iya gano ko daya daga cikin mutane 64 da aka tsare da sunan 'yan Boko Haram ba ne.
Kalli bidiyon da muka samo daga jaridar SaharaReporters:
Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama
A wani labarin, majiyoyin tsaro, a ranar Laraba, sun bayyana cewa sojojin da aka tura yankin Kuje da kewayen magarkama, wadanda suka yiwa yankin farin sani, an sauya musu mazauni sa’o’i 24 kafin ‘yan ta’adda su kai hari gidan yarin Kuje.
Majiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa aka kwashe su jami'an da suka san yankin sa'o'i 24 kafin harin, kuma har yanzu ba a samun wasu da suka maye gurbinsu ba har 'yan ta'addar suka far wa yankin, inji Vanguard.
Sai dai kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wa'adin da ya kamata sojojin su zauna a wannan yankin ya wuce kuma dama ya kamata a sauya su.
Asali: Legit.ng