Da dumi-dumi: Fitacciyar 'yar fim ra fito a a matsayin 'yar takarar mataimakin gwamna

Da dumi-dumi: Fitacciyar 'yar fim ra fito a a matsayin 'yar takarar mataimakin gwamna

  • Jam'iyyar PDP ta ba fitacciyar 'yar fim din Kannywood tikitin takarar kujerar mataimakiyar dan takarar gwamnan Legas
  • A wurin tantance ta, Funke Akindele Bello ta bayyana cewa, ita shahararriya ce, kuma za ta za ta kawo kuri'u da yawa
  • A baya dai Akindele ta fito neman takarar gwamna, amma abubuwa ba su tafi yadda ta tsara ba, ta rasa tikiti

Jihar Legas - An zabi Funke Akindele, ‘yar wasan fina-finan Nollywood da aka fi sani da ‘Jenifa’ a matsayin abkiyar takarar dan takarar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar PDP a Legas.

Ta zama ‘yar takarar mataimakin gwamna, inda ta doke wasu mutane biyar da suka nemi wannan mukami.

Wasu majiyoyi da dama na kusa da dan takarar gwamnan na PDP, Dr Abdul Azeez Olajide Adediran da aka fi sani da Jandor, da kuma shugabancin jam’iyyar a jihar, sun tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

Funke Akindele Bello ta zama abokiyar takarar Jandor
Da dumi-dumi: Fitacciyar 'yar fim ra fito a a matsayin 'yar takarar mataimakin gwamna | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An tattaro cewa za a bayyana Jenifa a matsayin abokiyar takarar Jandor a wani taron da za a yi nan ba da dadewa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta ruwaito yadda aka tantance sunayen mutane biyar da za su tsaya takarar.

Sun hada da Ms Akindele; tsohuwar 'yar takarar gwamna, Gbadebo Rhodes-Vivour; tsohon dan takarar Sanata mai wakiltar Legas ta Gabas, Yeye Shobajo, wani dan takarar gwamnan, David Kolawole Vaughan da aka fi sani da DAKOVA da Engr. Teslim Balogun.

Hoton Jandor da Akindele ya fara yaduwa yana nuna cewa an zabi jarumar ta Nollywood a matsayin abokiyar takararsa.

Sai dai an samu turjiya sosai daga wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, lamarin da ya janyo tsaiko wajen kammala zaben wanda zai tsaya takara tare da Jandor, inji BluePrint.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro ya sa masarautar Katsina ta dakatar da hawan Sallah

Daily Trust ta gano cewa, ‘yar takarar ta samu nasarar shawo kan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda ta yi nuni da irin farin jinin da Jenifa ke da shi a tsakanin matasa da kuma yadda ta fito daga yankin Sanatan Legas ta GabasIkorodu.

Wata majiyar kusa da dan takarar gwamnan ta tabbatar da zaben Ms Akindele amma ta kara da cewa "ba a sanar da ita a hukumance ba."

Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

A wani labarin, dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ribas, Dokta Innocent Barikor, ya tsallake rijiya da baya a wani harin da aka kai masa a Fatakwal, babban birnin jihar.

Sai dai an tattaro cewa, ‘yan bindigar sun kashe ‘yan sandan da ke bayansa nan take, inji rahoton The Nation.

An ce Barikor ya bar ofishinsa da ke GRA ne a daren ranar Talata domin wani taro a wani wuri da ba a bayyana ba ba tare da sanin cewa wasu ‘yan bindiga na jiransa a waje ba.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.