Harin gidan yarin Kuje: Fursunoni sama da 300 sun tsere
- A ranar Talata, 5 ga watan Yuli ne wasu yan bindiga suka kai farmaki gidan gyara hali na Kuje da ke babban birnin Abuja
- Wata majiya ta ce fursunoni sama da guda 300 ne suka gudu daga gidan yarin bayan yan bindigar sun samu shiga cikin cibiyar
- Maharan dai sun ta harbi sannan sun yi amfani da bama-bamai wajen samun iko kan hanyoyin shiga da fita daga cibiyar guda hudu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Rahotanni sun kawo cewa fursunoni sama da guda 300 ne suka tsere daga babban gidan gyara hali na Kuje da ke babbar birnin tarayya Abuja.
Hakan ya biyo bayan farmakin da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kai gidan gyara halin a daren ranar Talata, 5 ga watan Yuli.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wata majiya ta gidan yari da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewar fiye da fursunoni 300 ne suka tsere a yayin harin yan bindigar.
Majiyar ta yi ikirarin cewa maharani sun yi amfani da bama-bamai wajen samun karfin iko a wuraren shiga da fita guda hudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shashin BBC Pidgin ya rahoto cewa daya daga cikin jami’an ma’aikatar cikin gida ya ce rundunar tsaro sun daidaita lamarin, amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Hakazalika rahoton ya ce ana hasashen wasu adadi na fursunoni sun tsare daga cibiyar.
Ana tsoron ‘Yan bindiga sun aukawa gidan yarin Kuje, inda DCP Abba Kyari su ke daure
A baya mun kawo cewa a yammacin Talata, 5 ga watan Yuli 2022, wasu mutane da ba a san su wanene ba, sun kai hari a babban gidan gyaran hali na Kuje a garin Abuja.
Rahoton da Punch ta fitar ba da dadewa ba, ya tabbatar da cewa wasu mazauna Kuje sun ji karar fashewar wani abin mai kama da bam a yankin Shetuko.
Zuwa lokacin da aka tattara rahoton, jaridar ta ce ba ta iya gano abin da ya jawo wannan harin ba. Ana zargin cewa ‘yan bindiga ne suka kawo hari a yankin.
Asali: Legit.ng