Kamafanin simintin dangote ta bayyana shirin yadda zata samar da attajirai 25 a kowani wata
- Kamafanin Simintin Dangote ta kaddamar da tallar gasar biliyan daya ga kwastomominta dan samar da attajirai akalla ashirin da biyar 25 a kowani wata
- Kamfanin Siminti Dangote zata ba kwastomominta damar lashe kyaututtuka kamar na'urorin talabijin, firiji, fanka mai caji, janareta 2KVA, da kuma miliyoyin katin wayoyin sadarwa
- Kamfanin Simintin Dangote ta ce zata gudanar da tallar garabasar kyaututuka na tsawon watanni hudu
Jihar Legas- Kamafanin Simitin Dangote ta ce akalla mutane ashirin da biyar za su iya zama miloniya a cikin wata daya a wata gasar talla da ta ware Naira biliyan daya N1b mai taken “Spell Dangote and become a multi-millionaire.” Rahoton Jaridar PUNCH
Tallan wanda aka kaddamar a jihar Legas A ranar Talata tare da halartar jami’an hukumar kula da gasar da Caca na Najeriya NERC ana sa ran za ta bayar da kyaututtukan da za su canza rayuwan kwastomomin da za su yi wannan gasar ta hanyar siyan simintin kamfanin kamar yadda jaridar NewsNgr.com ta rawaito.
A cewar kamfanin, Dangote Cement Bag of Goodies Promo Season 3, wanda ke gudana daga Yuli 5 zuwa 31 ga Oktoba, 2022, zai ba abokan ciniki damar samun kyaututtuka kamar na'urorin talabijin, firiji, fanka mai caji, janareta 2KVA, da kuma miliyoyin katin waya na duka kamfanonin sadarwa a Najeriya.
Kamfanin tace, za a sanya katin kyaututtuka daban-daban a cikin kowani buhun Simintin Dangote a kowani rana na tsawon lokacin da za a gudanar da gasar wanda kwastomomin su ne za su lashe kyaututtukan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rashin tsaro: Sarkin Katsina ya dakatar da Hawan Sallar Idi
A wani labarin, Jihar Katsina - Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da hawan Daushe a lokacin bikin sallar Eid-el-Kabir da za a gudanar a ranar Asabar. Rahoton Daily Nigeria
Dakatawar ta fito ne a jawabin da mataimakin sakataren majalisar masarautar jiha, Sule Mamman-Dee ya fitar a ranar Talata inda ya ce an dakatar da bikin ne saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a fadin jihar.
Asali: Legit.ng