Hotuna: Matashin da ya tsinta jariri a titi shekaru 4 da suka wuce, ya saka shi makaranta

Hotuna: Matashin da ya tsinta jariri a titi shekaru 4 da suka wuce, ya saka shi makaranta

  • Wani matashi mai karancin shekaru ya labarta a kafar sada zumuntar TikTok yadda ya tsinci jinjiri a gefen titi shekaru hudu da suka shude
  • Daga lokacin matashin ya zama tamkar uwa da uban yaron, inda ya fara daukar ragamarsa tare da taimakon mahaifiyarsa
  • Bayan wasu shekaru, mutumin ya wallafa hotunan jinjirin a baya da na yanzu; harda wanda ke nuna ranarsa ta farko a makaranta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani matashi mai karancin shekaru mai amfani da shafin @kala_kakapentoa ya nuna halin tausayi da jin kai wanda ya dace mutane su yi koyi da shi.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafin, mutumin ya hada hotunan jinjirin a ya tsinta a jefen titi bayan shekaru hudu.

Mutumin ya bayyana yadda da taimakon mahaifiyarsa ya iya rainon yaron.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Abj-Kd: Shehu Sani da iyalan fasinjojin da aka sace zasu fito zanga-zanga

Kind Man
Hotuna: Matashin da ya tsinta jariri a titi shekaru 4 da suka wuce, ya saka shi makaranta. Hoto daga TikTok/@kala_kakapentoa
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, rainon jinjiri aiki ne mai matukar wahala.

A bidiyon, ya bayyanawa mutane yadda jinjirin ya girma ya zama yaron 'dan shekaru hudu. Yaron ya yi matukar kayatar wa yayin da aka masa askinsa na farko. Akwai hotunan mutumin rike da yaron.

Jama'a sun yi masa martani

Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a:

@kerenikwu100 ya ce: "mahaifiyata ta tsinci wata zankadediyar yarinya shekarun baya. Yanzu shekarunta tara, amma har yanzu tana tunanin mamana ta haifeta. Muna matukar kaunarta."
@ego_oyibo1802 ta ce: "Irin alherin da zai bika ko, babu dakin da zai iya daukar shi. Ubangiji ya muku albarka da karamin yaron."
@banxis1ofakind ta ce: "Nima ina da yaron da ba ni na haifa ba, bai da mai kula dashi saboda haka na daukesa kamar nawa. Wannan yaron zai zama maka alheri ka yarda da maganata."

Kara karanta wannan

Bidiyon Bahaushe gangaran a harshen Ibo ya girgiza intanet, ya sanyawa 'yarsa Ngozi

@athena04_6 ta ce: "Ina rokonka idan ya girma kada ka fada masa a gefen titi ka tsince shi. Ubangiji ya albarkaci zuciyarka."

Ba sai kun biya ba: Matukin adaidaita sahu dake daukan masu juna biyu kyauta ya birge jama'a

A wani labari na daban, wani matukin keke napep ya matukar taba zukatan mutane da kyan halinsa da ya bayyana inda 'yan Najeriya a kafar sada zumuntar zamani suka dinga kwarara masa yabo da addu'o'i.

Wani 'dan Najeriya mai suna Afrosix AJ Jaara ya wallafa abinda ya gani rubuce a cikin keken da ya shiga a shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel