PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

  • Jam'iyyar PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kira Buratai ya dawo gida daga jamhuriyar Benin
  • Kamar yadda takardar da Debo Ologunaba ya fitar, yace akwai zargin dake nuna Buratai ya kwashe wasu daga cikin kudin makamai da suka yi batan-dabo
  • PDP tace tana tare da 'yan Najeriya kuma babban laifi ne sace kudin makaman da aka ware domin yaki da ta'addanci a kasar nan

Jam'iyyar PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kira tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya kuma jakaden Najeriya a jamhuriyar Benin, Lt Janar Tukur Buratai.

A wata takardar da kakakin jam'iyyar, Debo Ologunaba ya fitar, jam'iyyar tace a binciki Buratai kan zargin alaka da N1.8 biliyan da ICPC ta samu a wani gida a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

Laftanal Janar Tukur Buratai mai ritaya
PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

PDP ta bukaci bincikar Buratai kan zargin NSA Janar Monguno, bayan tafiyar janar Buratai na cewa an kwashe dala biliyan daya daga lalitar gwamnati karkashin mulkin APC domin yaki da ta'addanci amma an kasa gano inda suka shiga.

Jam'iyyar tace zargin da NSA din ya fitar ya kara tabbatar da zargin da ake na cewa ana sace kudin makamai, inda suka kara da cewa "irin wannan rashawar karkashin gwamnatin APC ta janyo karuwar ta'addanci, kisan mutane da rashin manyan zakakuran sojoji dake gaba a yaki da rashin tsaro a shekaru bakwai da suka gabata."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babbar jam'iyyar adawan ta kara da ruwaito yadda shugabannin APC da masoyansu ke sace kudade a ma'aikatun gwamnati da cibiyoyinta, inda ta kwatanta mulkin APC da "daular barayin kasa".

"Bugu da kari, fallasar sace N80 biliyan ta dakataccen akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, wanda ake bincika ya yi sanyi yanzu, wanda ake zargin ya samu goyon bayan masu juya kasar da wasu jiga-jigan mulkin APC.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

"Jam'iyyar PDP na tare da 'yan Najeriya kuma tana jaddada cewa Buratai ya dawo kasar tare da fuskantar bincike domin dawo da sunansa.
"Saboda duk wani zargi da ya jibanci satar kudin yaki da ta'addanci babban lamari ne. Dole ne a bincike shi da kyau tare da duk wanda aka kama da hannu a hukunta shi komai mukamin shi," jam'iyyar tace.

Tsohon sojan da ya guje daga Maiduguri ya shiga hannu saboda hannu a fasa gidan yarin Imo

A wani labari na daban, rundunar ’yan sanda reshen jihar Imo ta ce ta kama wani mai suna Godwin Chukwuemeka, tsohon sojan da ake zargi da hannu a harin da aka kai cibiyar gyara tarbiyyar ta Imo.

A ranar 5 ga Afrilu, wadansu ’yan bindiga suka far wa cibiyar gyara halayyar da helkwatar ’yan sanda da ke Owerri inda Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya (NCS) ta ce fursunoni 1,844 suka tsere daga gidan.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

A ranar Litinin, Mike Abatam, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga kwamishinan ’yan sanda na jihar, ya gabatar da wanda ake zargin, inda ya ce ya amsa yana daga cikin ’yan bindigar da suka kai hari gidan yarin da kuma helkwatar ’yan sanda da ke Owerri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng