Tsohon sojan da ya guje daga Maiduguri ya shiga hannu saboda hannu a fasa gidan yarin Imo

Tsohon sojan da ya guje daga Maiduguri ya shiga hannu saboda hannu a fasa gidan yarin Imo

  • Mutumin ya amsa yana da hannu a fasa gidan yarin Owerri a watan Fabrairu
  • An same shi da bindigogi da alburusai iri-iri
  • Ya amsa cewa ya gudu daga aikin soja saboda halin tsaro a Arewa maso Gabas

Rundunar ’yan sanda reshen jihar Imo ta ce ta kama wani mai suna Godwin Chukwuemeka, tsohon sojan da ake zargi da hannu a harin da aka kai cibiyar gyara tarbiyyar ta Imo.

A ranar 5 ga Afrilu, wadansu ’yan bindiga suka far wa cibiyar gyara halayyar da helkwatar ’yan sanda da ke Owerri inda Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya (NCS) ta ce fursunoni 1,844 suka tsere daga gidan.

A ranar Litinin, Mike Abatam, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga kwamishinan ’yan sanda na jihar, ya gabatar da wanda ake zargin, inda ya ce ya amsa yana daga cikin ’yan bindigar da suka kai hari gidan yarin da kuma helkwatar ’yan sanda da ke Owerri.

Abatam ya ce an sami wanda ake zargin ne da kayan sarki na soja da takalmin ratsa hamada da kuma makamai, rahoton TheCable.

KU KARANTA: Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu

Tsohon sojan
Tsohon sojan da ya guje wa yaki da Boko Haram ya shiga hannu saboda hannu a fasa gidan yarin Imo hoto:decencyglobal
Asali: UGC

KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

Yace:
"Bayan samun sahihan bayanai, sai rundunar 'yan sandar Imo ta mamaye maboyar wani sanannen mai laifi a yankin Owerri Nekede, inda aka kama wani mai suna Godwin Chukwuemeka, wanda aka fi sani da Match and Die, mai shekara 35, a cikin silin din gidansa.
“Ana zargin cewa mutumin cewa soja da aka kora daga bakin aiki. A lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa yana daga cikin wadanda ake zargin kai hari a helkwatar rundunar 'yan sanda ta Jihar Imo da kuma cibiyar gyara, da ke Owerri, a farkon wannan shekarar.
“A halin yanzu, an kwato wadannan abubuwa daga wanda ake zargin: karamar bindiga da wata karamar bindiga mai sarrafa kanta da albarussai masu rai guda biyu da harsashi daya marar rai da kakin sojoji da takalmin soja na ratsa hamada.

Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin, Chukwuemeka ya ce ya tsere ne daga sansanin sojoji da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar nan saboda tashe-tashen hankula masu nasaba da Boko Haram a yankin.

An damke dan sanda mai safarar makamai

Wani Sufeton ‘yan sanda, Nathaniel Manasseh, ya shiga hannun 'yan sanda a Jihar Kuros Riba bisa zargin dillancin bindigogi da alburusai ga masu aikata laifuka.

An cafke Manasseh a Calabar, babban birnin jihar, kuma aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda ranar Talata tare da sauran wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, an ce shi babban dillalin bindiga ne kuma ya dade yana wannan harkallar kafin dubunsa ya cika.

Sufeton da ya amsa laifin shi, an ce shi ne ke kula da ma'ajiyar makamai a rundunar 'yan sanda ta jihar kuma an kama shi ne lokacin da ya kasa ba da bahasin wasu kayan aiki ciki har da bindigogin AK-47 guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel