Yajin aiki: Yau kwanaki 140 Ɗalibai na zaman gida, SERAP da wasu sun soki FG
- A yau Litinin 4 ga watan Yuli, ɗalibai suka shiga kwana na 140 a gida tun bayan fara yajin aikin ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU
- Ƙungiyar SERAP da wasu ƙungiyoyin ilimi a Najeriya, sun caccaki gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
- Ƙungiyoyin sun nuna sakacin FG da ƙin cika alƙawari ne suka jawo rufe harkokin ilimi a manyan makarantu
Abuja - Ƙungiyar Socio-Economic Rights Accountability Project (SERAP) da wasu ƙungiyoyin fafutuka kan ilimi a Najeriya, sun caccaki gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan rufe harkokin karatun makarantun gaba da Sakandire na tsawon lokaci.
Punch ta rahoto cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta tsunduma ya shiga kwana na 140 yau Litinin, yayin da yajin aikin manyan ma'ikata da kanana na jami'o'i ya shiga kwana na 68.
Yayin da yanzu haka shugabannnin ƙungiyar kwalejin fasa ke gudanar da taro a Jigawa bayan janye yajin aikin gargaɗi na mako biyu, ƙungiyar malaman kwalejin ilimi sun tsunduma yajin aikin watanni biyu.
A wata sanarwa da ta fito ranar Lahadi, mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, yace gazawar FG na cika bukatun ASUU, ƙin aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar ya bar 'ya'yan talakawa a gida yayin da yan siyasa suka tura yaran su makarantun kuɗi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Oluwadare ya ce:
"Rashin daidaito a ɓangaren ilimi ya haifar da sakamako mai illa, kuma ga dukkan alamu a haka za'a cigaba har gaba. Bayan kasancewarsa dama a karan kansa, samun damar yin ilimi makulli ne ga wasu damarmakin."
"Ilimi ke samar da murya wacce ake fafutukar kare haƙƙi da dama, idan babu ilimi mutane ba zasu iya cimma wasu abubuwa masu amfani ba da suka shafi rayuwa."
"Idan mutane suka samu ilimi, za su yi amfani da kwarewa da kwarin guiwa wajen kwato haƙƙoƙin su. Ilimi na baiwa mutane karfin samun bayanai kan nauyin da ya rataya kan gwamnati."
Wasu ƙungiyoyin ilimi biyu sun bi sahun SERAP baya
Da yake jawabi a wata hira da wakilin mu ranar Lahadi, shugaban ƙungiyar fafutukar gyara ilimi a Najeriya, Ayodamola Oluwatoyin, ya soki shirun manyan masu ruwa da tsaki game da rufe harkokin karatu.
Oluwatoyin ya ce:
"Abun takaici ne gwamnati ta kama hannunta ta bari ana tattaunawar da babu alamar sasantawa. Wajibi fadar shugaban ƙasa cikin gaggawa ta karɓi ragamar tattauna wa da ƙungiyoyin nan."
Haka nan kuma, shugaban ƙungiyar Education Rights Campaign, Michael Lenin, ya ce: "Wajibi a ɗora laifin wannan yajin aikin kungiyoyin wanda ya dakatar da harkokin ilimi a wuyan gwamnati."
"Abu ne da bamu saba gani ba cewa dukkan manyan ƙungiyoyin makarantun gaba da Sakandire suna yajin aiki; hakan ya nuna yadda gwamnatoci masu biye wa juna suka ɓarnata ɓangaren ilimi ta fannin kuɗi."
Sabon rikici ya ɓarke a PDP, Babban Jigo ya yi watsi da Atiku, yace wajibi mulki ya koma kudu a 2023
Wane hali ake ciki game da yajin aikin?
Duk wani yunkuri na jin ta bakin ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, bai yi nasara ba. Ngige ya ayyana ƙanshi a matsayin ministan sasanci tsakanin FG da ƙungiyoyin.
Da aka tuntuɓi shugaban ƙungiyar malamai kwalejojin fasaha, Dr. Anderson Ezeibe, ya ce majalisar shugabannin ƙungiyar zasu fara zama ranar Talata.
"NEC zata fara zama ranar Talata, idan ba mu gamsu da matakin da aka ɗauka na cika mana buƙatun mu ba, zamu tsunduma yajin aiki."
Haka nan ba'a samu shugaban ƙungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ba yayin da aka nemi jin ta bakinsa da yammacin lahadi.
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin SSANU, NASU da NAAT, Muhammed Ibrahim, bai ɗaga kiran salula da aka masa ba kuma be turo amsar saƙonni ba.
A wani labarin kuma Ɗan majalisar tarayya da mambobin PDP sama da 18,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a jiha ɗaya
'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai
Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ta shiga babban rikici a jihar Oyo yayin da dubbannin mambobinta suka rungumi APC.
Ɗan majalisar tarayya, Muraina Ajibola, ya jagoranci mambobi sama da 18,000 sun koma APC daga PDP.
Asali: Legit.ng