A Zurfafa Bincike Kan Yaran Musulmi 21 Da Aka Ceto a Cocin ECWA Plateau, In Ji MURIC

A Zurfafa Bincike Kan Yaran Musulmi 21 Da Aka Ceto a Cocin ECWA Plateau, In Ji MURIC

  • Kungiyar Musulunci Ta MURIC ta bukaci Babban Sifetan Yan Sanda da shugaban DSS sun duba batun yara musulmi da aka ceto a wani gidan coci a Plateau
  • Farfesa Ishaq Akintola, shugaban kungiyar ta MURIC ne ya yi wannan kiran cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Farfesa Akintola ya nuna matukar mamakinsa kan zargin da aka yi na cewa tilastawa yaran aka yi zuwa gidan aka sauya musu addini kan dole

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi, MURIC, ta bukaci Sufeta Janar Na Yan Sanda, IGP, da Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, DSS, ta bincike yadda aka gano tare da ceto yara musulmi 21 a wani gini mallakar cocin ECWA a Jos, Jihar Plateau.

Farfesa Ishaq Akintola.
A Yi Bincike Kan Yaran Musulmi 21 Da Aka Ceto a Cocin Plateau, MURIC. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shugaban MURIC na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan jiran cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Damfara Ta N26.7m: Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Maka Mataimakin Kwamandan NSCDC a Kotu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa a baya-bayan nan ne DSS ta kai samame wani gida da ke JMDB quaters a unguwar Tudun Wada a karamar hukumar Jos ta Arewa, inda jami'an suka ceto yaran musulmi 21.

An yi ikirarin cewa an da karfi da yaji aka kai yaran gidan kuma aka sauya musu addini zuwa kiristanci.

Sakatare Janar na ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu, shima ya tabbatar da cewa gidan da aka gano yaran da abin da ya faru da su mallakar cocin ne.

MURIC ta bayyana 'mamakinta kan zargin aikata laifi' bayan gano yaran ta kuma bukaci a gudanar da cikakken bincike.

Jam’ian DSS sun ceto Almajirai 21 da aka turke a Cocin ECWA ana kokarin mayar da su Kirista a Jos

Tunda farko kun ji cewa Jam’ian hukumar DSS sun kai samame wani gida da ke JMDB quarters, unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Jos ta Arewa inda ta ceto yara 21, cikinsu har da Almajirai.

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI ya laburtawa manema labarai cewa yaran sun yi bayanin yadda aka garkamesu cikin gidan ana kokarin tilastasu komawa addinin Kirista, rahoton Daily Trust.

Sakataren cocin ECWA, Rabaran Yunusa Nmadum ya tabbatar lallai gidan da DSS ta kai samame mallakin cocinsa ne amma ya musanta cewa ana amfani da gidan wajen tilasta mutane shiga addinin Kirista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164