Bama tilasta wa Almajirai shiga addinin Krista - Cocin ECWA

Bama tilasta wa Almajirai shiga addinin Krista - Cocin ECWA

  • Cocin Evangelical Winning All (ECWA) ta karyata zargin da ake mata na tilasta Almajirai shiga addinin kristanci a Filato
  • Shugaban cocin ECWA ya ce labarin canzawa almajirai addinin su yunkuri ne na bata sunan cocin su
  • Cocin ECWA ta ce duka yaran dake hannun su manya ne wanda babu wanda ya gaza kasa da shekara goma sha takwas

Jihar FILATO : Cocin Evangelical Winning All (ECWA) ta karyata zargin da ke mata na sauya wa Almajirai adinnin su na musulunci zuwa addinin Krista.

ECWA ta bayyana haka ne yayin da take mayar da martani kan labarin yadda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kubutar da wasu matasan musulmai 21 da aka canza musu addini zuwa Kristanci. rahoton jaridar Daily Trsut

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

A wata zantawar da shugaban cocin, Rabaran (Dr) Stephen Baba Panya yayi da jaridar Daily Trust, ya ce zargin da ake yiwa ECWA wani yunkuri ne na bata sunan Cocin da gangan.

vanguard
Bama tilasta wa Almajirai shiga addinin Krista - Cocin ECWA
Asali: UGC

Shugaban cocin yace,

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

”Sauran bangarorin cocin ECWA sun kadu da suka ji karyar da aka musu wanda ya fito daga bakin wani matashi da ya tsere daga hannun su mai suna Abdulrahaman Hussaini, akan suna tilasta musu shiga adinin Krista a inda suke musu horon koya aikin hannu.
“Wannan zargin karya ne kuma sauran yaran da muke horras wa suna nan, jami’an gwamnati za su iya musu tamboyoyi, kamar yadda jami’an DSS suka yi musu dan binciko gaskiyar al’amarin.
“Duka wandanda muke horras wa, manya ne wanda babu daya daga cikin su da ya gaza kasa da shekara sha takwas (18), kuma suna da damar ficewa idan dokokin mu basu musu ba inji shi”.

Kara karanta wannan

Zabe: INEC ta shiga damuwa kan yadda ba a karbar katunan zabe gabanin 2023

Daily Trust a ranar Litinin ta ruwaito yadda kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Filato ta ba da labarin yadda wadanda abin ya shafa suka ce an kawo su gidan da karfi kuma ana tilasta musu shiga addinin Krista.

Kotu ta yanke wa yan luwadi hukuncin kisa a jihar Bauchi

Babbar kotun shariar musulunci dake jihar Bauchi ta yanke wa wasu matasa biyu da dattijo hukuncin kisa ta hanyar jefewa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022. bisa laifin yiwa wasu kananan yara luwadi.

Kotun ta samu mutanen, wanda suka hada da matasa biyu da kuma wani dattijo mai misalin sheakru 70, da wannan kazamin laifi, wanda dukkanin su suka amsa aikata lafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa