Kano: Kotu Ta Hana Ganduje Ciyo Bashin Naira Biliyan 10 Don Siyo CCTV Kyamara

Kano: Kotu Ta Hana Ganduje Ciyo Bashin Naira Biliyan 10 Don Siyo CCTV Kyamara

  • Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano ta dakatar da Gwamna Abdullahi Ganduje daga ciwo bashin N10bn don siyan CCTV Kyamara da wasu na'urorin tsaro
  • Hadakar kungiyoyi masu zaman kansu karkashin Kano First Forum, KFF, ne ta yi ƙarar Gwamna Ganduje da Antoni Janar na Kano da Kwamishinan Kuɗi da wasu kan batun
  • KFF ta yi zargin cewa gwamnatin na Jihar Kano ta saɓa wasu dokokin karbo bashi don hakan ta ke son kotun ta hana a ciyo bashin da Majalisar Jihar ta amince a ciyo tun a ranar 15 na Yunin 2022

Kano - Wata kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Abdullahi Liman, a ranar Juma'a ta hana gwamnatin Jihar Kano ciyo bashin Naira biliyan 10 don saka kyamaran tsaro na CCTV da wasu kayan tattara bayanan tsaro, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: INEC ta bayyana wanda ta amince ya yi takarar gwamna a PDPa jihar Kano

Hadakar kungiyoyi masu zaman kansu, NGOs, mai suna Kano First Forum, KFF, ce ta shigar da kara a ranar 27 ga watan Yuni, ta hannun direktan kungiyar, Dr Yusuf Isyaka-Rabiu.

Gwamna Ganduje
Kano: Kotu Ta Hana Ganduje Ciyo Bashin Naira Biliyan 10 Don Siyo CCTV Kyamara. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KFF, ta hannun lauyoyinsu, da Badamasi Suleiman-Gandu ke yi wa jagoranci, ta roki kotun ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ciyo bashin na Naira biliyan 10.

Wasu da aka hada cikin karar sun hada da Antoni Janar na Kano, Kwamishinan Kuɗi da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar.

Saura sun hada da wani bankin zamani, ofishin kula da bashi da hukumar sa ido kan yadda ake kashe kudade.

Mai shari'a Liman ya amsa rokon KFF ya hana wanda aka yi ƙarar na farko daga karbo bashin na N10bn ya kuma umurci sauran suma su dakata da maganan.

Ya kuma umurci wanda ya yi ƙarar ya mika wa Ma'aikatar Kudi na Tarayya, Ofishin Kula da Bashi da Hukumar sa ido kan yadda ake kashe kudi da sauran takardan umurnin kotun.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

Ba a bi ka'idoji ba wurin ciyo bashin, in ji KFF

KFF na kallubalantar Gwamnan Jihar Kano bisa karbo bashin na N10bn da cewa ba a bi ka'idojin karbo bashi ba.

Masu shigar da karar sun kallubalanci gwamnatin jihar ta ƙin bin dokar 'Dept management office establishment Act 2003 da fiscal responsibility Act na 2007 da dokokin jihar Kano na 1968, don haka bai hallarta a karbo bashin ba.

Za a sanar da ranar cigaba da sauraron shari'ar nan gaba.

A ranar 15 ga watan Yuni ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje na karbo bashin N10bn daga wani bankin zamani a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164