Zaben 2023: Ba Zan Yi Wa INEC Katsalandan Ba, In Ji Buhari
- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta sakarwa hukumar zabe INEC mara ta yi aikinta yadda ya dace a zaben 2023
- Buhari, yayin ganawarsa da yan Najeriya mazauna kasar Portugal a birnin Lisbon ya bada misali da zabukan gwamnonin Anambra da Ekiti yana mai cewa mutane su zabi wanda suke so
- Shugaban na Najeriya ya kuma gargadi yan Najeriya mazauna kasashen waje su guji amfani da kafafen sada zumunta wurin tunzura mutane ko zagi da cin mutunci
Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jadada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta yi zabe na adalci kuma cikin zaman lafiya a 2023.
Ya bada tabbacin cewa ba zai yi wa INEC katsalandan ba, yana mai cewa bayan kammala zaben cikin gida na jam'iyyu, yanzu an sa ido ne kan zaben 2023 a Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buhari, a cewar sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter, ya yi magana ne a daren ranar Laraba a Lisbon yayin ganawarsa da yan Najeriya da ke zaune a Portugal.
"Muna fatan ganin an mika mulki ga gwamnati na gaba ba tare da tangarda ba. Kamar yada na fada a baya ba za mu yi kasa a gwiwa wurin yin abin da ya dace ba don walwalar yan Najeriya na gida da waje," in ji shi.
Buhari, wanda ya bada misali da zaben gwamna da aka yi a jihohin Ekiti da Anambra ya ce gwamnatinsa ta nuna cewa ba za ta amince da yi wa hukumar zabe katsalandan ba, yana mai cewa a kyalle yan Najeriya su zabi jam'iyya da dan takarar da suke so.
Ya kuma yi gargadin a dena amfani da dandalin sada zumunta don tunzura mutane ko zagi daga nesa ko badda kama.
Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari
A wani labarin, Festus Keyamo SAN, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, yace matsin lamba da yan uwa da abokanai ke yiwa mutane masu rike da mukami ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.
A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.
Asali: Legit.ng