Bayan shekaru 8, wata ‘Yar Chibok ta kubuta daga hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram

Bayan shekaru 8, wata ‘Yar Chibok ta kubuta daga hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram

  • Rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar sake gano wata daga cikin daliban makarantar Chibok
  • Sojoji sun ce an ceto wannan yarinyar ne a jihar Borno, har yanzu ana kokarin yin bincike game da ita
  • Manjo Janar Christopher Musa ya bada wannan sanarwa da kan sa a madadin Operation Hadin Kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Dakarun sojoji na Operation Hadin Kai sun ce sun ceto wata daga daliban makarantar nan ta garin Chibok da ‘yan ta’addan Boko Haram suka dauke.

Rahoton da Channels TV suka fitar da rahoto a yammacin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, an ceto yarinyar nan ne a yankin Bama da ke jihar Borno.

Shugaban Rundunar Operation Hadin Kai na kasa, Manjo Janar Christopher Musa ya bada wannan sanarwa da ya yi magana da wasu manema labarai.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Janar Christopher Musa ya shaida cewa ana bincike a kan wannan Baiwar Allah da aka ceto domin samun cikakken bayani a game da ita, da yankin ta fito.

Ba samu bayanin yarinyar ba

Da zarar sojoji sun kammala bincikensu, ana sa ran za su bayyana wannan yarinya, su tuntubi iyayenta. A al’ada, kwararrun likitoci za su duba lafiyarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan ake sa rai sojojin za su damka wanda aka ceto ga iyayenta ko dai wasu na kusa da ita.

Sojoji
Gasar Sojoji na NASAC 2022 a Filato Hoto: @NigerianArmy
Asali: Facebook

Ba yau aka fara ba

Kamar yadda gidan talabijin ya fitar da labarin, ba wannan ne karon farko da sojoji suka yi kokarin gano wasu daga cikin daliban makarantar Chibok ba.

A Afrilun 2021 ne aka ji Gwamnan Borno Babagana Zulum ya yi alkawarin kubutar da ragowar yaran. An gano wasunsu, amma har yau wasunsu ba su dawo ba.

Kara karanta wannan

Borno: Bidiyo ya nuna lokacin da 'yan Boko Haram 314 ke mika wuya ga jami'an sojoji

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan yarinya da ire-irenta da ke hannun ‘Yan kungiyar Boko Haram sun shafe fiye da shekaru takwas a hannun ‘yan ta’addan a jeji.

Tun a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, ‘yan ta’addan na Boko Haram suka shiga makarantar sakandaren gwamnati da ke Chibok, suka sace yara fiye da 200.

Mai karyar an sace ta

Ana da labari cewa an yi shari’a tsakanin Ameerah Sufyan da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a wani kotun majistare a kan karyar da ta yi na cewa an dauke ta.

Da aka zauna a gaban Alkali, Ameerah Sufyan ta amsa laifuffukan da ake zargin ta. Alkali ta yi hukunci cewa sa'ilin da ta yi wannan aiki, ba ta cikin hayyacinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng